Yadda wasu yara suka tuttule jarkan mai kacokan a kan motar iyayensu

Yadda wasu yara suka tuttule jarkan mai kacokan a kan motar iyayensu

- Wata fusatacciyar uwa, Bongiwe Malunga, ta wallafa hotunan kananan yaranta da motar da suka lalata

- Bongiwe ta bayyana cewa za ta hukunta su ta hanyar soke kayan sabbin kayan kirisimetinsu

- Mabiya shafin Twitter sun yi sharhi kan wallafarta yayinda wasu suka nemi a sanya idanu sosai a kan yaran a koda yaushe

Duk da kasancewar yara abun sha’awa mafi akasarin lokuta sun iya barna idan ba a lura dasu ba. Wata uwa mai suna Bongiwe Malunga ta je shafin Twitter don nuna barnar da yaranta suka yi.

A wasu jerin hotuna da ta wallafa a yanar gizo, an gano yaran tsaye a gefen motan da jarkan mai.

A matsayin hukunci, matar ta bayyana cewa ba za ta yi wa yaran kayan bikin Kirsmeti ba.

Yadda wasu yara suka tuttule jarkan mai kacokan a kan motar iyayensu
Yadda wasu yara suka tuttule jarkan mai kacokan a kan motar iyayensu Hoto: @BIndlovukazi
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Za a samu tsaro idan yan siyasan Najeriya suka daina amfani da yan daba da miyagu, Yahaya Bello

Hotunansu ya janyo cece-kuce sosai daga iyaye da mutane a yanar gizo.

Kalli wallafarta a kasa:

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, wallafar mahaifiyar ya samu fiye da likes 40,000 da dubban sharhi.

Legit.ng ta tattaro wasu sharhi a kasa:

@SkedoKimZ ya ce:

“Kalle su kamar na kwarai yayinda suke ci gaba da tsayuwa a wajen aika-aikan da suka yi.”

@Observer_July ya ce:

“Amma fa laifinki ne na rashin adana man ta yadda ba za su gani ba. Toh da ace sun sha ne fa? Ko kuma su samu hanyar cinna masa wuta sannan su kona kansu?”

KU KARANTA KUMA: Masu garkuwa sun kai hari Kano, sace dan kasuwa sun kuma kone motar 'yan sanda

@Boipelo_Joy tayi martani:

“Yara sun wuce tunanin mutum kuma duk taka-tsan-tsan da mutum zai yi a koda yaushe suna da aika-aikan da za su yi."

A wani labarin, wata matashiyar budurwa mai hidimar kasa ta sa mahaifiyarta hawaye bayan wani jawabi mai ratsa zuciya da ta yi yayin da ta dawo daga sansanin masu hidimar kasa.

Matashiyar mai bautan kasan sanye da cikakkun kayan hidimar kasa, ta tattaka har zuwa gaban mahaifiyarta inda ta yi mata jinjina.

Kamar yadda matashiyar tace: "Jinjina kashi uku ga mahaifiyata wacce ita kadai ta raine ni, ta yi min tarbiya tare da tura ni makaranta har na kai matsayin hidimtawa kasata."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel