Dattijo mai shekaru 80 ya mutu a dakin Otal bayan shakatawa da matashiya 'yar 33

Dattijo mai shekaru 80 ya mutu a dakin Otal bayan shakatawa da matashiya 'yar 33

- An tsinci gawar David Mluli a ranar Asabara, 16 ga watan Janairu, a daki mai lamba 22 a Mbezi Garden, Dar es Salaam city

- An dauki gawarsa zuwa asibitin Mwananyamala don yi masa gwaji tare da gano dalilin mutuwarsa

- Jami’an tsaro sun ce sun tsinci KSh 1,750 (N6,042.42), katin shaidar zama dan kasa nasa da wayar Tecno bayan sun gudanar da binciki dakinsa

Wani tsoho dan shekara 80 ya mutu a wani lamari mai rikitarwa a wani masauki da ke Dar es Salaam, Tanzania, bayan ya shafe dare da wata matashiya mai shekara 33.

An tsinci David Mluli matacce a ranar Asabar, 16 ga watan Janairu, a daki mai lamba 22 a Mbezi Garden, inda ya je shakatawa da wata mata mai suna Neema Kibaya (33) wacce tuni aka kama ta kan mutuwarsa.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: FG tayi amai ta lashe, ta ce bata yarda da bude makarantu a ranar 18 ga Janairu ba

Dattijo mai shekaru 80 ya mutu a dakin Otal bayan shakatawa da matashiya 'yar 33
Dattijo mai shekaru 80 ya mutu a dakin Otal bayan shakatawa da matashiya 'yar 33 Hoto: Richard Vako.
Asali: Facebook

Kwamandan yan sandan yankin Kinondoni, Ramadhan Kinai ya tabbatar da labarin bakin cikin kamar yadda The Citizen ta ruwaito.

Shugaban yan sandan ya ce:

“Yan sanda sun isa yankin sannan suka tsinci gawar Mista Mluli tare da wata mata wacce ta bayyana kanta a matsayin Neema Kibaya. Kibaya ya fada ma yan sandan batun alaka ta soyayya da ke tsakaninta da marigayin.”

Jami’an sanye da inifam sun dauki gawar mamacin zuwa asibitin Mwananyamala don yin gwaji saboda gano abunda ya haddasa barinsa duniya.

KU KARANTA KUMA: Hadimar gwamna tayi murabus domin tsiratar da aurenta, ta mika wasikar ajiye aiki

Ba a zargin wani abu

A bisa ga binciken fari, babu wani abu da ake zargi kuma ta iya yiwuwa Mluli ya yi mutuwar Allah ne.

Kingai ya bayyana:

“Babu wani alamu da ke nuna kokwanto kan haka ill an gano gajeren bujensa a jike kafin ya mutu.”

A wani labari na daban, wata hadimar Gwamnan jihar Ebonyi tayi murabus daga gwamnatin.

Hadimar wacce kafin murabus dinta take a matsayin babbar mai bayar da shawara ga gwamnan kan ci gaban kasuwanci ta bayyana dalilinta na ficewa daga gwamnatin.

A wasikar murabus dinta mai kwanan wata Laraba, 30 ga watan Disamba, 2020, wanda Legit.ng ta gano, Deaconness Udeakaji ta bayyana cewa murabus din nata ya zama dole domin tsiratar da aurenta.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng