Bidiyon da ke nuna wasu yan damfara suna watsa bandir din kudi a kogi ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya

Bidiyon da ke nuna wasu yan damfara suna watsa bandir din kudi a kogi ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya

- Bidiyon wasu yan Najeriya ya shahara a shafin soshiyal midiya inda aka gano su suna watsa bandir din kudi a kogi

- Mazajen sun wanke fuskokinsu a cikin ruwan kazantan wanda masu amfani da shafin sadarwar ke ganin asiri suke yi da nufin habbaka arzikinsu

- Daya daga cikin wadanda suka yi martani kan bidiyon ya ce a koda yaushe iblis kan wahalar da wanda ya mallakawa dukiya

Wani bidiyo ya shahara a shafin soshiyal midiya na wasu da ake zaton yan damfara ne suna watsa bandir din kudi a kogi.

Yan Najeriya a shafin soshiyal midiya na ganin cewa abunda suka aikata asiri ne da nufin bunkasa arzikinsu.

A bidiyon, an gano mazan su hudu suna wanke fuskokinsu a cikin ruwan kazanta.

Bidiyon da ke nuna wasu yan damfara suna watsa bandir din kudi a kogi ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya
Bidiyon da ke nuna wasu yan damfara suna watsa bandir din kudi a kogi ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya Hoto: @lindaikejiblogofficial
Source: Instagram

KU KARANTA KUMA: Kudu ya kamata mulki ya koma a 2023, Gwamnan Borno Zulum

Yan Najeriya sun je shashin sharhi na bidiyon wanda @lindaikejiblogofficial ta wallafa a Instagram.

@officialbecks ta ce:

“Suna biyan shaidan bashin abunda yake nashi.”

@iamvictoria_richard ta ce:

“Idan arzikinka ba na Allah bane, shaidan zai ta wahalar da kai a koda yaushe.”

@angelsvirginhair_ ta rubuta:

“Ta Yaya hakan ya zama asiri?? Allah ya kyauta. Kamar yadda kuka yarda da Annabi Isah sannan kuke zuwa coci da sadaka, sauran ma suna da nasu al’adan da suke ba abun bautar su. Wannan ba tsafi bane.”

KU KARANTA KUMA: Wani gwamnan Nigeria zai mutu, shahararren fasto ya yi gargadi a wahayin 2021

A wani labarin, wani Shugaban addini, Apostle Paul Okikijesu na cocin Christ Apostolic Miracle Ministry ya yi ikirarin cewa Allah ya bayyana masa cewa wani gwamnan Najeriya zai mutu a 2021.

Okikijesu wanda yayi ikirarin a wani wahayi da ya saki na sabuwar shekaara ya ce mutuwar gwamnan namiji zai ba mace damar zama gwamna.

Sai dai malamin bai bayyana jihar Najeriya da hasashensa zai fada a kai ba. Ya kuma yi ikirarin cwa Allah ya bayyana masa cewa za a yi gagarumin rikici a Aso Rock.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel