Bola Tinubu
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi magana kan zanga-zangar da ake yi a fadin kasar nan. Ya ce ya kamata gwamnonin Arewa su farka su yi abin da ya dace.
Wasu mabarata a Kano sun roki jagororin da su ka shirya zanga-zanga su yi hakuri, su janye saboda su samu damar fitowa neman na kai wa bakunansu.
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya ce tsare-tsaren Bola Tinubu a Najeriya su suka jefa al'umma cikin mawuyacin hali inda ya bukaci ya sauya salo.
Malamin addini kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a APC Tunde Bakare ya yi kira ga yan siyasa kan bukatar talakawa, ya ce ba wanda ya dauki nauyin zang zanga.
Dan majalisar wakilai Uchenna Harris Okonkwo ya yi kira ga Bola Tinubu kan shawo kan damuwar talakawa maimakon yin magana kawai, ya ce ana wahalar rayuwa.
Ministan harkokin noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya shawarci 'yan Najeriya da su hakura da zanga-zangar da suke yi kan halin kunci a kasar nan.
Kasashen Amurka da Burtaniya sun bayyana damuwa kan rashin da aka yi yayin zanga-zanga inda suka bukaci Bola Tinubu ya tattauna da matasan domin shawo kan matsalar.
Sarkin Idjerhe a jihar Delta, Obukowho Monday Whiskey ya goyi bayan shugaban kasa na neman tattaunawa da masu zanga-zanga, inda ya ce hakan zai magance matsalolin.
Shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Abdullahi Ganduje ya yi magana kan halin kunci da 'yan kasar ke ciki wanda ya tilasta zanga-zanga a birane da dama.
Bola Tinubu
Samu kari