Bola Tinubu
An samu labarin yadda aka raba Naira Biliyan 438 tsakanin Gwamnoni 34 da Ministan Abuja, Nyesom Wike. Zamfara ta samu N49bn amma ba a ba Kaduna ko sisi ba
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da wani bangare na aikin babbar hanyar Kano zuwa Maiduguri saboda sakaci na 'yan kwangila da bata lokaci a aikin na tsawon lokaci.
Jam'iyyar APC reshen jihar Kano, ta buƙaci a gudanar da bincike kan zargin karkatar da shinkafar gwamnatin tarayya a Kano. Ta zargi wasu jami'an gwamnati.
Shugaban cocin INRI Spiritual Evangelical Church, Primate Elijah Babatunde Ayodele, ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sallami Mele Kyari daga mukaminsa.
Aminu Abdullahi Chubado ya yi tir da yadda aka cusa riba a tallafin gwamnatin tarayya. Ko da ruwan 1% ne, musulmai za su kyamaci cin irin wannan bashi saboda addini.
Tsohon gwamna Kano, Malam Ibramin Shekarau ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da tawagarsa su sake zama kan matakan da ya ɗauka tun da ya hau mulki.
Dan Bello na ganin ya wayar da kan jama’a, wasu su na zargin ya kawo abubuwan da babu tabbas a cikin bidiyoyin na sa har ana kira cewa ya kamata a cafke shi.
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana cewa za su cigaba da zama da kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso domin dawowa ECOWAS inda ya ce za su inganta tsaro.
Mataimakin shugaban kasar, Kashim Shettima ya bayyana shirye-shiryen Bola Tinubu kan matasa inda sha alwashin cigaba da tafiya da su a wannan gwamnati.
Bola Tinubu
Samu kari