'Yan Majalisa Sun Tsige Kakakin Majalisar Dokoki Saboda Wasu Zarge Zarge

'Yan Majalisa Sun Tsige Kakakin Majalisar Dokoki Saboda Wasu Zarge Zarge

  • Ƴan majalisar dokokin jihar Cross Rivers sun ɗauki matakin tsige kakakin majalisar, Elvert Ekom Ayamben daga muƙaminsa
  • Ƴan majalisa 17 ne suka tsige Elvert Ekom daga kan muƙaminsa a ranar Laraba, 22 ga watan Mayun 2024 a zauren majalisar dokokin ta jihar Cross Rivers
  • Bayan tsige kakakin dai an so a ba hammata iska a tsakanin ƴan majalisar bayan wani saɓani da ya ɓarke a tsakaninsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Cross Rivers - Ƴan majalisar dokokin jihar Cross Rivers sun tsige kakakin majalisar, Honorabul Elvert Ekom Ayambem daga muƙaminsa.

An tsige kakakin ne daga kan muƙaminsa a ranar Laraba, 22 ga watan Mayun 2024 bayan an zarge shi da yin watanda da kuɗin al'umma.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS da ƴan sanda sun mamaye zauren majalisa yayin da rigama ta kaure

An tsige kakakin majalisar dokokin jihar Cross Rivers
'Yan majalisa sun tsige kakakin majalisar dokokin jihar Cross Rivers Hoto: @makesensepromot
Asali: Twitter

An tsige shugaban majalisar dokoki

Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa ƴan majalisar mutum 17 ne suka goyi bayan kuɗirin tsige kakakin daga muƙaminsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Honorabul Effiom Ekarika wanda ke wakiltar mazaɓar Calabar ta Kudu 1, shi ne ya gabatar da ƙudirin, sannan Honorabul Omang Charles Omang, mai wakiltar mazabar Bekwarra ya mara masa baya.

Elvert Ayambem wanda yake wakiltar mazaɓar Ikom 2 an zaɓe shi a matsayin kakakin majalisar dokokin ne a ranar 10 ga watan Yunin 2023.

Wa'adin mulkinsa ya zo ƙarshe inda ko shekara ɗaya bai yi ba a kan kujerar saboda zarge-zargen da ake yi masa.

An ba hammata iska a majalisa

Rahoton tashar Channels tv ya bayyana cewa an yi hargitsi a majalisar bayan an tsige Elbert Ayambem.

Ɗaya daga cikin ƴan majalisar ya yi yunƙurin ƙwace sandar majalisar wacce ke nuna alamar ikon kakakin majalisar.

Kara karanta wannan

'Dan majalisa ya faɗi yadda suka shirya tsige sarakuna 5 da Ganduje ya naɗa a Kano

Sai dai, ɗan majalisar da yake ɗauke da sandar ya ƙi yarda da hakan, lamarin da ya jawo aka nemi ba hammata iska a zauren majalisar.

An tsige kakakin majalisar dokokin Ogun

A wani labarin kuma, kun ji cewa Yan Majalisar jihar Ogun sun tsige kakakin Majalisar, Kunle Oluomo kan wasu zarge-zarge da dama.

Ƴan majalisa 18 ne daga cikin mambobin majalisar 36 suka zabi tsige kakakin majalisar yayin zaman da suka yi a ranar Talata 23 ga watan Janairun 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng