Yan ta'adda
Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi arangama tsakanin Kungiyar Boko Haram tsagin Bakoura da ISWAP a Abadam da ke jihar Borno a Arewacin Najeriya.
Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Gombe sun samu nasarar cafke wasu mambobin kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram. An cafke su ne a cikin wani otal.
'Yan ta'addan Boko Haram da ISWAP sun yi kare jini biri jini da suka gwabza fada a jihar Borno. An kashe da dama cikin 'yan ta'addar a kusa da kasar Nijar.
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya bukaci rundunar sojin saman Najeriya da ta cigaba da sintiri a iyakokin jihar domin maganin 'yan ta'adda.
Dan majalisar tarayya a Amurka, Scott Perry, ya zargi hukumar USAID da taimaka wa kungiyoyin ta'adda, ciki har da Boko Haram da ke addabar Arewa maso Gabas.
Gwamnonin Kudu maso Yamma sun kafa tawagar hadin gwiwa ta tsaro tare da amfani da fasahar zamani don tabbatar da tsaro da bunkasa tattalin arzikin yankin.
Gwamnatin tarayya da hadin gwiwar gwamnatin Zamfara sun kaddamar da shirin sauya tunanin 'yan bindiga a Arewa ta Yamma. Za a karbi 'yan ta'adda da suka tuba.
Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da zaman lafiya sun samu nasarori kan 'yan ta'adda a jihohin Zamfara da Sokoto. Sojojin sun hallaka kwamandoji masu yawa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa fitaccen shugaban 'yan bindiga, Kachalla Dan Lukuti, ya rasu bayan fama da wata muguwar cuta da ta sa ya fara yin haushin kare.
Yan ta'adda
Samu kari