Yan ta'adda
An yi bata gari da dama da suka addabi Najeriya a zamani daban-daban, daga cikinsu akwai Abubakar Shekau na Boko Haram, Lawrence Anini, Oyenusi da sauransu.
Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki cikin ƙauyen Ejule ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kwara. Ƴan bindingan sun salwantar da rayukan mutane masu yawa a harin.
Wasu mahara da ake kyautata zaton yan ta'adda ne sun yi ajalin rayukan mutane sama da 10, sun kona gidaje da Coci a yankin karamar hukumar Mangu, jihar Filato.
Tawagar jami'an tsaro wacce ta ƙunshi ƴan sanda da ƴan sakai tare da mafarauta ta tarwatsa maɓoyar ƴan bindiga tare da halaka wasu daga cikinsu a jihar Katsina.
Yanzu muke samun labarin yadda wasu tsageru suka hallaka matashin yaro a jihar Bauchi yayin da suka kai hari wata kasuwa a cikin birnin Jama'are da ke jihar.
Dakarun sojin saman Najeriya sun samu nasarar sheƙe mayaƙan ƙungiyar ta'addancin ISWAP tare da kwamandojinsu a wani farmaki da suka kai maɓoyarsu a jihar Borno.
Wasu miyagun mahara sun halaka babban basaraken Fulani da ke a wani ƙauye a ƙaramar hukumar Zaria cikin jihar Kaduna. Maharan sun kuma halaka ƴaƴansa guda huɗu.
Ƴan bindiga sun halaka wasu manoma biyu a ƙauyen Unguwar Gajere cikin ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna a wani sabon hari da suka kai zuwa yankin.
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce wadanda suka kafa kungiyar Boko Harama a arewa sun fada masa cewa talauci da rashin aikin yi ne ya jefa su a halin.
Yan ta'adda
Samu kari