Kwamandan ISWAP Ya Sheka Barzahu Bayan Maciji Ya Sare Shi

Kwamandan ISWAP Ya Sheka Barzahu Bayan Maciji Ya Sare Shi

  • Wani babban kwamandan ƙungiyar ta'addanci ta ISWAP ya sheƙa barzahu bayan maciji ya sare shi a cikin dajin Sambisa
  • Kwamandan mai suna Kiriku dai ya baƙunci lahirar ne kwanaki uku bayan macijin mai mugun dafi ya sare shi
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa Kiriku wanda ya sha kai hare-hare kan dakarun sojoji ya mutu ne bayan ya kasa samun magani

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Borno - Wani babban kwamandan ƙungiyar ta'addanci ta Islamic State of West African Province (ISWAP), mai suna Kiriku ya baƙunci lahira a dajin Sambisa.

Kiriku ya mutu ne bayan wani maciji mai mugun dafi ya sare shi a cikin dajin Sambisa na jihar Borno.

Babban kwamandan ISWAP ya sheka barzahu a jihar Borno
Kwamandan ya mutu ne bayan sarin maciji Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

An tattaro cewa Kiriku ya sha sarin macijin ne mai guba wanda yake da kalar launin ruwan ƙasa a maɓoyarsu da ke a masallacin Agikur cikin ƙaramar hukumar Damboa, ranar Talata sannan ya mutu a ranar Juma'a, 23 ga watan Yunin 2023.

Kara karanta wannan

Nasara Daga Allah: Hatsabiban 'Yan Ta'adda 6 Sun Sheƙa Lahira a Arewacin Najeriya

Zagazola Makama, wani masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi ya rahoto cewa ɗan ta'addan ya sheƙa barzahu ne a dalilin rashin samun kayan aikin da za a duba lafiyarsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya daɗe yana addabar jami'an tsaro

Kiriku yana ɗaya daga cikin kwamandojin ƙungiyar da su ke gudanar da ta'addancinsu a yankin Jiddari na Chiralia a cikin Timbuktu waɗanda suka sha kai hare-hare akan jami'an tsaro.

Ɗan ta'addan tare da wasu kwamandojin ƙungiyar sun sha kai kwanton ɓauna a kan dakarun tsaron Operation Hadin Kai a tsakanin hanyar Maiduguri zuwa Damboa.

An daɗe ana rikicin ta'addanci a jihar Borno

Matsalar rikicin ta'addanci a jihae Borno ba ta yanzi bace domin rikicin ya shafe sama da shekara 10 ana tafka shi, inda ƙungiyoyin ta'addanci na ISWAP da Boko Haram ke fafatawa da jami'an tsaro.

Kara karanta wannan

Sabon Shugaban Rundunar Sojin Najeriya Ya Kama Aiki Gadan-Gadan, Ya Ɗauki Manyan Alkawurra

Ayyukan ta'addancin dai sun salwantar da rayukan mutane da dama da dukiyoyinsu, yayin da wasu mutanen da dama suka rasa matsugunansu.

Zulum Ya Yi Allah Wadai Da Harin ISWAP

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya nuna takaicinsa kan kisan gillar da ƴan ta'addan ISWAP suka yi wasu manoma a jihar.

Gwamnan ya sha alwashin ɗaukar tsatstsauran mataki domin hana sake aukuwar hakan a nan gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel