'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki a Jihar Kogi, Sun Halaka Mutane Da Dama

'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki a Jihar Kogi, Sun Halaka Mutane Da Dama

  • Miyagun ƴan bindiga sun kai wani mummunan a farmaki cikin tsakar dare a wani ƙauye cikin jihar Kogi
  • Ƴan bindigan sun kai farmakin ne a cikin ƙauyen Ejule da ke a ƙaramar hukumar Ofu ta jihar a daren ranar Alhamis
  • Ana fargabar mutane da dama sun rasa rayukansu a harin inda aka gano gawar mutum biyu daga cikin waɗanda suka rasu

Jihar Kogi - Wasu ƴan bindiga sun farmaki ƙauyen Ejule a cikin ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi inda suka halaka mutane da dama.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa harin ya fara da misalin ƙarfe 3:00 na daren ranar Alhamis.

'Yan bindiga sun kai farmaki a jihar Kogi
Ana fargabar 'yan bindigan sun halaka mutane da dama Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Rahotanni sun tabbatar da wani ɗan Achaɓa da matar wani shugaban matasa a garin sun baƙunci lahira a harin.

Kara karanta wannan

Rashin Daraja: Magidanci Ya Maka Surikansa Kara a Gaban Kotun Shari'ar Musulunci a Jihar Kano Kan Abu 1 Rak

Harsashi ne ya samu ɗan Achaɓan yayin da matar tana tsaka da neman mijinta ne lokacin da harbin ya iso kanta inda nan ta ke tace ga garinku nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma ƴan bindigan sun ƙona wani gida a yayin da suka kai a ƙauyen.

Wani mazaunin garin ya bayyana cewa:

"Ba zan iya faɗin adadin mutanen da suka mutu ba. An gano biyu daga cikinsu, ɗaya ɗan Achaba yayin da ɗayar matar wani shugaban matasa ce na garin."
"Har yanzu ƙura bata lafa ba, amma an ga gawarwaki a bakin hanya. Babu wanda zai iya fitowa waje yanzu."

Na kusa da gwamna ya tabbatar da aukuwar harin

Mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Kwamanda Jerry Omadara (mai ritaya), ya tabbatar da aukuwar amma ya bayyana cewa bai samu cikakkun bayanai ba dangane da harin.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Mummunan Hari a Arewa, Sun Banka Wa Mutane Sama da 10 Wuta Har Lahira

Ya zuwa ƙarfe 9:30 na safiyar ranar Alhamis rahotanni sun nuna cewa mutane basu fito daga cikin gidajensu ba yayin da wasu kuma suka arce suka bar garin.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP William Aya, bai ɗauki kiran wayar da aka yi masa ba lokacin da aka so jin ta bakin shi.

'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Da Matarsa a Jihar Kogi

A wani labarin na daban kuma, ƴan bindiga sun yi awon gaba da Oba na Odofin da matarsa suna cikin tafiya a ƙaramar hukumar Yagba ta Gabas a jihar Kogi.

Ƴan bindigan sun ɗauke Shedrack Durojaiye Obibeni da mao ɗakinsa ne lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa wata unguwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel