Gwamna Zulum Ya Nuna Takaicinsa Kan Kisan Manoma a Borno, Ya Bayyana Kwakkwaran Matakin Da Zai Dauka

Gwamna Zulum Ya Nuna Takaicinsa Kan Kisan Manoma a Borno, Ya Bayyana Kwakkwaran Matakin Da Zai Dauka

  • Gwamnan jihar Borno ya nuna takaicinsa kan mummunan harin da ƴan ta'addan ISWAP suka kai kan wasu manoma a jihar Borno
  • Ƴan ta'addan dai sun halaka wasu manoma takwas a ƙaramar hukumar Mafa suna tsaka da ayyukansu a gonakinsu
  • Gwamnan ya sha alwashin samar da tsaro ga manoma domin tabbatar da cewa sun ci gaba da ayyukansu ba tare da fargaba ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya nuna takaicinsa kan kisan manoma takwas da ƴan ta'addan ISWAP suka yi a ƙaramar hukumar Mafa ta jihar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rahoto cewa harin ya auku ne a Shuwarin, Tomsu Ngamdu, Baram Karauwa da Muna a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 1:00 na rana lokacin da manoman su ke aiki a gonakinsu, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Manyan Jiga-Jigan PDP da Dubannin Mambobi Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC Ana Tunkarar Zaɓe a Jihar Arewa

Gwamnan Zulum ya yi Allah wadai da kisan manoma a Borno
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Gwamna Zulum, wanda ya ziyarci Mafa domin miƙa ta'aziyyarsa ya bayyana harin a matsayin abin takaici.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta haɗa hannu da jami'an tsaro domin tura ƙarin sojoji su kula da tsaron gonakin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Gwamnatin jiha za ta kira taron gaggawa na majalisar tsaro domin samar da hanyoyin ganin an samar da wadataccen tsaro ga manoma." A cewarsa.

Gwamnatin jihar za ta kafa tawagar jami'an tsaro ta musamman

Zulum ya kuma bayyana cewa za a kafa wata tawaga ta musamman wacce za ta haɗa da ƴan sibil difens, sojoji, ƴan sakai da mafarauta domin kare manoman, rahoton Channels tv ya tabbatar.

Ya bayyana matsalar rashin abinci za ta fi matsalar Boko Haram zama babban rikici, inda ya yi nuni da cewa gwamnatin jihar za ta yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da mutane sun samu damar zuwa gonakinsu.

Kara karanta wannan

Nasara Daga Allah: Hatsabiban 'Yan Ta'adda 6 Sun Sheƙa Lahira a Arewacin Najeriya

Dakarun Sojin Najeriya Sun Sheke 'Yan Ta'addan ISWAP Guda 6 a Jihar Borno

A wani labarin na daban kuma, dakarun sojin Najeriya sun samu nasarar sheƙe mayaƙan ƙungiyar ta'addanci ta Islamic State of West Africa Province (ISWAP) a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun halaka ƴan ta'addan ne su shida a ƙaramar hukumar Bama ta jihar. Ƴan ta'addan da aka sheƙen suna da matuƙar haɗari saboda su ne masu dasa bama-bamai akan hanya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng