Yan ta'adda
Malamin Musulunci a jihar Sokoto, Sheikh Bello Yabo ya karyata rade-radin cewa yan bindiga sun yi garkuwa da shi da kuma cewa hukumar DSS ta cafke shi.
A wannan rahoton, shugaban majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas ya bayyana takaicin yadda yan bindiga su ka sace wasu ma'aikatan jinya a jihar Kaduna.
Yayin ake zargin Bello Matawalle da hannu a ta'addanci, gamayyar malaman Musulunci daga Arewacin Najeriya sun goyi bayan yaki da ta'addanci na gwamnatin Bola Tinubu.
Gwamna Dikko Umaru Radda ya amince da ba mutane izinin mallakar bindiga domin yakar yan ta'adda. Mutanen Arewa za su mallaki bindiga domin kare kansu.
Sheikh Bello Yabo ya ce ko zai yi gaba da gaba da yan bindiga ba zai daina musu nasiha ba. Bello Yabo ya ce bai yarda yan bindiga za su iya galaba a kansa ba.
Alkalin babbar kotun jihar Borno da 'yan ta'adda suka yi garkuwa da shi, Haruna Mshelia, ya kubuta. Alkalin ya kubuta ne bayan ta kwashe watanni biyu a tsare.
Rundunar sojojin Najeriya a Jalingo ta ce ta samu nasarar kama wata matashiya da ke kaiwa 'yan bindiga bayanai kuma ana zargin budurwar dan bindiga 'Chen' ce.
Rahotanni sun bayyana cewa an cimma matsaya tsakanin mazauna kauyen Moriki da ke Zamfara da Bello Turji cewa 'yan kauye za su biya diyyar N30m na kashe shanunsa.
Rahoto ya bayyana cewa kimanin mutane 13,346 aka kashe yayin da aka sace wasu 9,207 daga hawan Shugaba Bola Tinubu kan mulki zuwa watan Satumbar 2024.
Yan ta'adda
Samu kari