Mai Rabon Ganin Badi: Yan Bindiga Sun Saki Yaran Alkaliya da Aka Sace a Kaduna

Mai Rabon Ganin Badi: Yan Bindiga Sun Saki Yaran Alkaliya da Aka Sace a Kaduna

  • Bayan shafe kwanaki 15 a tsare, masu garkuwa da mutane sun saki yaran alkaliya da suka sace a jihar Kaduna
  • 'Yan ta'adda sun sace alkaliyar kotun gargajiya, Janet Galadima da yaranta guda hudu a ranar 23 Yuni, 2024
  • Daga baya su ka sake ta, sannan aka kashe babban danta Victor saboda gaza biyan kudin fansa da ya kai Naira Miliyan 150

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Bayan shafe kwanaki 15 a hannun masu garkuwa da mutane, yaran mai Shari'a Janet Galadima sun shaki iskar 'yanci.

Shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa (NBA), reshen jihar Kaduna, Godwin Ochai ne ya tabbatar da sakin yaran.

Kara karanta wannan

Auren jinsi: Yadda kururuwar mutanen Kano ya dakile yunkurin kungiyar LGBTQ

Kaduna map
'Yan ta'adda sun saki sauran yaran alkaliya Janet Galadima Hoto: Legit Nigeria
Asali: Original

Jaridar Leadership ta wallafa cewa 'yan ta'adda sun sace alkaliya Janet da yaranta hudu a ranar 23 Yuni, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Alkaliya na tare da yaranta," NBA

Shugaban kungiyar lauyoyi reshen jihar Kaduna, Godwin Ochai ya ce yanzu haka Janet Galadima na tare da sauran yaranta, Daily Trust ta wallafa.

Bayan sace alkaliyar kotun gargajiya da yaranta dai 'yan bindiga sun kashe babban danta, Victor mai shekaru 14 saboda gaza biyan kudin fansa.

Daga baya su ka sako Janet Galadima, amma sun hana sauran yaran guda uku inda su ka ce sai an biyasu kudin fansa Naira Miliyan 150.

Kungiyar lauyoyin ta godewa dukkanin wadanda su ka taya su addu'a har sauran yaran su ka kubuta.

An biya kudin fansa?

Duk da cewa 'yan ta'addan tun farko sun nemi kudin fansa, amma kungiyar NBA ba ta ce komai kan batun ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon shugaban kungiyar NLC, an samu bayanai

Legit Hausa ta tuntubi jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya ce da zarar bincike ya kammala zai yi mana karin bayani.

Kaduna: An sace tsohon shugaban NLC

A baya mun kawo labarin cewa 'yan ta'adda sun kai hari jihar Kaduna inda suka sace tsohon shugaban NLC, Takai Agang Shamang.

Rahotanni sun bayyana cewa an sace Mista Shamang mai shekaru 73 har gidansa da ke Bikini-Tsoraurang, Manchock, karamar hukumar Kaura.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.