Ke Duniya: An Kama Wani Mutum da Zargin Kashe Mahaifiyarsa Mai Shekaru 100 a Najeriya

Ke Duniya: An Kama Wani Mutum da Zargin Kashe Mahaifiyarsa Mai Shekaru 100 a Najeriya

  • Al’ummar wani yanki a jihar Osun sun shiga firgici bayan da wani mutum ya yiwa mahaifiyarsa tsohuwa kisan gilla
  • Mutumin mai suna Lukman Adejoju ya kashe mahaifiyarsa da aka ce tana da shekaru kusan 100 a duniya saboda kudin manja
  • Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta tabbatar da afkuwar lamarin tare da kama Lukman Adejoju, da kuma wadanda suka taya shi barnar

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Osun - Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Osun sun kama wani mutumin mai suna Lukman Adejoju bisa zargin kashe mahaifiyarsa dattijuwa mai suna Aminat.

Jaridar Punch ta ruwaito a ranar Lahadi, 14 ga watan Afrilu cewa Lukman, mazaunin kauyen Kajola ne da ke kusa da Apomu a jihar Osun.

Kara karanta wannan

Rudin soyayya: Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da jami'inta ya kashe mace mai ciki

An kama wanda ya kashe mahaifyarsa a kan manja
Kudin manja ya sa wani ya kashe mahaifiyarsa | Hoto: GettyImages, NPF (Facebook)
Asali: UGC

Meye dalilin da yasa ya kasha mahaifiyarsa?

Rahoton ya bayyana cewa mutumin ya kashe mahaifiyarsa, wadda aka ce tana da shekaru kusan 100 a duniya, sakamakon takaddamar da ta shiga tsakaninsu kan manja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani ganau mai suna Rasaki ya bayyana a ranar Lahadi cewa Lukman da mamaciyar sun dauki wani lebura ne wanda ya taimaka musu wajen siyar da wasu jarakunan manja.

Yayin da leburan ya dawo masu da kudin, an ruwaito marigayiya Aminat ta dage cewa sai dai a ba ta kudin kudin, lamarin da ya harzuka dan nata Lukman, The Eagle Online ta tattaro.

Yadda rikicin ya fara har ta kai ga sabani

Ya ci gaba da cewa:

“Mazauna kauyen duk sun ji takaici da muka samu labarin faruwar lamarin. Lamarin ya faru ne a kauyen Kajola da ke kusa da Apomu ranar Asabar da misalin karfe 4:00 na yamma.

Kara karanta wannan

Gaba da gabanta: Jami'in dan sandan da ya yi barazanar sheke farar hula da bindiga ya shiga hannu

“Mun ji cewa Lukman wanda ya kai kimanin shekara 63 ya samu sabani da mahaifiyarsa Aminat mai shekara 100, kan wanda zai karbi kudaden da suka samu daga manjan.”

Matashi ya kashe mahaifiyarsa a Kano

A wani labarin, kun ji yadda wani matashi ya yi amfani da makami wajen kisan mahaifiyarsa a jihar Kano.

Matashin mai suna Ibrahim Musa, an ce ya kashe mahaifiyar tasa mai shekaru 50 ne a Rimin Kebe da ke karamar hukumar Ungogo da ke jihar.

Ya zuwa lokacin hada rahoton, an kama matashin kuma za a dauki mataki a kansa bayan bincike, kamar yadda hukuma ta bayyana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel