Yan ta'adda
Matashiya yar TikTok a jihar Sokoto, Hamdiyya Sidi Shareef ta fadi abubuwan da suka faru da ita bayan fitar da wani bidiyo da ake zargin ta ci mutuncin gwamna.
Sojojin Najeriya sun fafata da yan ta'addar IPOB a jihar Imo. Sojojin sun kashe da dama cikin yan IPOB bayan sun yi gaba da gaba da yan ta'addar a wani fada.
Ana fargabar yan kungiyar Lakurawa sun fara yaɗuwa a jihohin Kaduna da Niger, rundunar sojoji za ta sake tura dakaru yankunan domin kawo karshensu.
Rundunar yan sanda a jihar Kano ta kama hatsabibin dan dabar unguwar Ɗorayi da ake nema ido rufe. An kama Auwal ɗan daba ne bayan an dauki lokaci ana nemansa.
Rundunar yan sanda ta cafke miyagu da yan ta'adda 523 a cikin watanni biyu a jihar Kaduna. An ceto mutane 102 daga hannun masu garkuwa da mutane a Kaduna.
An harbe ango ana shirin daura masa aure a ranar Jumu'a. Amarya ta gigice saboda harbe angon da ake hasashen yan kungiyar asiri ne suka harbe shi har lahira.
'Yan ta'adda sun halaka kimanin mutane 30 tare da raunata sama da mutane 37 a garuruwan jihar Benuwai. An ce 'yan ta'addan sun kona gidaje da sace kayayyaki.
Rundunar yan sanda ta yi musayar wuta da yan bindiga masu garkuwa da mutane a karamar hukumar Jibia inda ta ceto mutane 14, daya ya rasu saboda harbi
A wannan rahoton, za ku ji cewa rundunar sojin Nijar ta bayar da tabbacin cewa dakarunta sun hallaka wasu daga cikin 'yan ta’addan Lakurawa a yankin.
Yan ta'adda
Samu kari