"Turji Ya Tsorata": Malamin Musulunci Ya Dira kan 'Dan Ta'adda, Ya Kalubanci Matawalle

"Turji Ya Tsorata": Malamin Musulunci Ya Dira kan 'Dan Ta'adda, Ya Kalubanci Matawalle

  • Sheikh Murtala Bello Asada ya sake kalubalantar Bello Turji a wani bidiyo inda ya tabbatar da zargin ana daukar nauyin ta'addanci
  • Malamin ya ce Turji a faifan bidiyo, ya tabbatar da hannun karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle wajen harkar ta'addanci
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan kisan rikakken dan ta'adda, Halilu Sabubu a Zamfara a ranar Juma'a da ta gabata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Malamin Musulunci, Sheikh Murtala Bello Asada ya sake sakin bidiyo game da Bello Turji.

Shehin malamin ya ce tabbas Turji ya cika matsoraci wanda tun bayan mutuwar Halilu Sabubu ya koma Kagara.

Malamin Musulunci ya kalubanci Matawalle, ya fadi yadda Turji ya ke
Sheikh Murtala Bello Asada ya caccaki Bello Turji yayin da ya tabo Bello Matawalle. Hoto: Malam Murtala Bello Asada, Dr. Bello Matawalle.
Asali: Facebook

Bello Turji: Murtala Asada ya ja kunne

Kara karanta wannan

Badaƙalar N80bn: Yahaya Bello ya faɗi yadda ta kaya bayan ya miƙa kansa ga EFCC

Bello Asada ya fadi haka ne a bidiyo da hadimin gwamnan Zamfara, Mugira Yusuf ya wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin faifan bidiyon, Sheikh Asada ya kalubalanci Bello Turji ya fadi duk inda ya ke idan ya cika namiji kuma hatsabibi.

Wannan martanin malamin na zuwa ne bayan Turji ya saki sabon bidiyo da ya ke neman gafarar wadanda ya yi wa laifi.

Malamin ya ce Turji ya sake tona asirin wadanda ke daukar nauyin ta'addanci ciki har da karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle.

"Yau ga Bello Turji kaskance wanda ya ke ta shi da bindiga cikin izza amma ya yi kasa yana cewa duk wanda na yi wa laifi ya yafe mani."
"Na ce mun fadawa jami'an tsaro inda Turji yake ya tsorata ya yi hijira zuwa Kagara gidan kakanninsa ta bangaren uwa."

Kara karanta wannan

'Kowa na talaucewa' Malamin addini ya tura zazzafan sako ga Bola Tinubu

"Idan jarumi ka ke menene zai mayar da kai gida, bala'i za ka jawo musu, fitowa zaki yi a yi gaba da gaba da kai a daji."

- Murtala Bello Asada

Sheikh Bello Asada ya kalubanci Matawalle

Daga bisani malamin ya kalubalanci Bello Matawalle kan zargin daukar nauyin ta'addanci inda ya ce yana da hujjoji.

Malamin ya ce idan akwai mai kalubalantarsa kan zargin ya ke a fito a fada inda ya fadi tonon asiri da Turji ya yi a cikin faifan bidiyo.

Ya ce Turji ya fadi cewa sun kashe barayi, Matawalle ya dauki wasu daga cikinsu ya kai su gidan gwamnati ba tare da karbar makamansu ba.

Bello Turji ya gargadi Murtala Asada

A baya kun ji cewa dan ta'adda, Bello Turji ya sake fitar da bidiyo kan fitaccen malami, Murtala Bello Asada da Bulama Bukarti bayan fitar da wani rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda ya fadi lokacin gamawa da Turji, ya tona abin da ke rura wutar

Bello Turji ya bukaci Janar Christopher Musa ya ba Sheikh Asada mukami ko na shugabancin yan banga ne domin su gwabza.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.