Manyan 'Yan Ta’adda 5 da Suka Mutu a Arewa, daga Boko Haram zuwa 'Yan Bindiga

Manyan 'Yan Ta’adda 5 da Suka Mutu a Arewa, daga Boko Haram zuwa 'Yan Bindiga

Tun farkon fara ayyukan ta'addanci na Boko Haram zuwa yan bindiga, an yi manyan yan ta'adda a Arewacin Najeriya wanda wasu sun riga sun mutu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Arewa - Ayyukan ta'addancin Boko Haram kusan shi ne ya jawo yawaitar yan ta'adda a Arewacin Najeriya a baya bayan nan.

Haka zalika ɓullowar yan bindiga a Arewa ta Yamma ya kara haifar da yan ta'adda masu garkuwa da mutane da dama a Najeriya.

Yan ta'adda
Manyan yan ta'adda da aka kashe a Arewa. Hoto: @RFJ_USA (Adamu A Babale Makera|Facebook)
Asali: Twitter

Mun tattaro muku jerin manya daga cikin yan ta'addar wanda wasu jami'an tsaro ne suka kashe su, wasu kuma su suka kashe kansu ko abokan ta'addancinsu.

Kara karanta wannan

An cafke dan ta'adda mai nuna bindiga a intanet da gungun yan fashi a Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jerin yan ta'adda da suka mutu a Arewa

1. Muhammad Yusuf

Muhammad Yusuf ya kasance shugaban farko na kungiyar Boko Haram da ta fara ta'addanci a jihar Borno a Arewa maso gabas.

Shugaban Boko Haram, ya mutu ne bayan yan sandan Najeriya sun bude masa wuta a shekarar 2009 bayan an cafke shi.

2. Abubakar Shekau

Abubakar Shekau ya gaji Muhammad Yusuf shugabancin Boko Haram wanda shi ma ya jagoranci ayyukan ta'addanci.

Abubakar Shekau ya mutu ne a shekarar 2021 inda wasu rahotonni suke nuna shi ya kashe kansa a lokacin da yaga alamar zai mutu bayan sun yi fada.

3. Abu Mus'ab Albarnawi

Abu Mus'ab Albarnawi ya kasace ɗa ga shugaban Boko Haram Muhammad Yusuf kuma ya jagoranci kungiyar ISWAP.

Legit ta ruwaito cewa a shekarar 2021 rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa Abu Mus'ab ya mutu.

Kara karanta wannan

Malamin Musulunci ya yi bayani kan karbar tuban Bello Turji da sauran yan bindiga

4. Halilu Sabubu

Halilu Sabubu ya kasance cikin manyan yan bindiga da aka yi a Arewa ta yamma wanda ya jagoranci ayyukan garkuwa da mutane da renon yan ta'adda irinsu Bello Turji.

Legit ta wallafa cewa a watan Satumban 2024 ne rundunar sojin Najeriya ta kashe shi bayan wani kwanton ɓauna da aka masa tare da magoya bayansa.

5. Beleri Fakai

Baleri Fakai na cikin mayan yan bindiga da suke tare da Bello Turji wajen ayyukan ta'addanci a Arewa ta Yamma.

A watan Satumba ne sojoji suka kashe Baleri kamar yadda Legit ta ruwaito, duk da cewa wasu na fadin cewa yan ta'adda ne suka kashe shi a wani fada da suka yi.

Tinubu ya yabi sojoji kan kisan 'dan ta'adda

A wani rahoton, kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya nuna farin cikinsa kan nasarar da dakarun sojoji suka samu kan ƴan bindiga a yankin Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Sojoji sun bude wuta, an damke masu taimakon 'yan bindigan Arewa da makamai

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yabawa sojojin bisa nasarar da suka samu kan kisan babban shugaban ƴan bindiga, Halilu Sabubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng