Abun Bakin Ciki
Tsohon Sarkin Damaturu na farko, Alhaji Mai Aliyu Muhammad Biriri ya riga mu gidan gaskiya a kasar Saudiyya ya na da shekaru 82 a duniya bayan fama da jinya.
An kama wani malamin tsibbu a Ifa, Onifade Oyekanmi, bisa laifin hada baki da abokansa wajen kashe wata mata mai suna Usman Aminat a kan neman kudi a Ibadan.
Hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare ta JAMB ta dauki mataki kan jami’anta da suka ci zarafin wata daliba sanye da hijabi a Legas.
Akalla sojoji shida ne aka kashe a kauyen Karaga da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Neja bayan sun fada wani tarko da 'yan bindiga suka dana masu.
Gwamnatin jihar Kwara ta aika tawaga ta musamman wadda ta dura kasuwar Mandate da ke Ilorin inda suka kwace naman shanu da aka yi fargabar na dauke da guba.
Yayin da wasu kafafen yada labarai suka sanar da mutuwar tsohon gwamnan Oyo, Dakta Omololu Olunloyo ya ƙaryata rade-radin inda ya ce har yanzu ya na nan.
Al'ummar kauyen Sansani da ke karamar hukumar Gasol a jihar Taraba sun shiga ɗimuwa bayan 'yan bindiga sun hallaka Sarkin ƙauyen, Abdulmutalib Nuhu.
Rundunar sojojin Nigeriya ta tabbatar da cafke jami'anta guda biyu kan zargi sata a matatar Aliko Dangote da ke Legas inda ta ce yanzu haka ta na kan bincike.
Yayin da ake jimamin rasuwar Sanata Rafiu Ibrahim, an sanar da mutuwar mahaifin Sanata Sadiq Umar da ke wakiltar Kwara ta Arewa a Majalisar Dattawa.
Abun Bakin Ciki
Samu kari