KAI TSAYE: Yadda Aka Tashi Wasan Real Madrid da Barcelona

KAI TSAYE: Yadda Aka Tashi Wasan Real Madrid da Barcelona

Komai na iya faruwa a El Clasico

Real Madrid dai na da maki a teburin gasar kuma za ta iya dorawa kan nasararta a gasar La Liga, yayin da Barcelona ta samu cikas bayan shan kaye a wasanta da PSG.

Real za ta yi nasara ko da an tashi wasan da kunnen doki, amma Barca na bukatar maki uku. Yanzu da aka taken wasan, bari mu yi kallo muga abin da zai faru. Ku biyo mu sau da kafa.

Za mu bibiyi kafar yada labaran wasanni ta NBC Sport domin kawo maku wasan kai tsaye.

Real Madrid 0-1 Barcelona (Minti na 6)

Jarumin tsakiyar mako shine zakaran wasan farko. Farawa da iyawa har Barca ta zura kwallo daya a ragar Madrid.

Andriy Lunin, wanda ya yi fice sosai a Man City a tsakiyar mako, bai iya kai wa ga kwallo ba, amma Andreas Christensen ya tashi sama da Toni Kroos ya kai zura kwallon da ka.

Fenariti ga Real Madrid (Minti 18)

Vazquez ne ya ke rike da kwallo kusa da matashin tauraron Barca Pau Cubarsi ya bar kafarsa a kasa don kokarin hana wucewa.

Madadin hakan, Vazquez ya tabbatar ya yi tuntuɓe da ƙafar Cubarsi inda ya fadi, kuma an ba da bugun fanareti.

Vini ya zura kwallon. Yanzu muna 1-1.

Cikakken lokaci: Real Madrid 3-2 Barcelona

Madrid sun yi nasara. Sun zo ne daga baya sau biyu domin zama masu jan ragamar La Liga tare da dora hannu daya a kan kofin.

Real Madrid 3-2 Barcelona

Jude Bellingham ya yi bugun ƙafar hagu daga kusurwa, ƙila ba iya wasan ya ci ba har ma da La Liga!

An ba Modric kati

An nuna wa kyaftin din tawagar gida katin gargadi saboda ya taka Joao Felix.

An canja Vinicius Junior, bai ji dadi ba

Daren taka ledar dan wasan gaba na Brazil ya kare a wannan wasa. An ba shi katin gargadi 'yan mintoci kaɗan da suka gabata, wanda wataƙila ya ƙara sa wa aka fitar da shi.

Jules Kounde shi ma an ba shi katin gargadi saboda rawar da ya taka a wata arangama tsakanin 'yan wasan.

Real Madrid 2-2 Barcelona

Vinicius Junior ne ya mika kwallo ga Lucas Vazquez wanda yake can a shirin kai farmaki, kuma ya zura ta a raga.

El Classico ta ɗauki wani juyi kuma haka ma tseren kofin yake.

Real Madrid 1-2 Barcelona

Fermin ya dawo da martabar Barca kuma La Liga ta dauki mikati a tsakanin abokan hamayyar biyu.

Barcelona ta yi canji guda biyu

Joao Felix da Ferran Torres sun maye gurbin Robert Lewandowski da Raphinha.

Lallai wannan wasa ya dauki zafi

Barcelona na neman bugun fanareti

Fermin ya fadi a cikin gida yana neman fanareti.

Antonio Rudiger, wanda ya yi tadiyen bai nuna damuwa a kai ba.

Mafi mahimmanci, alkalin wasan bai nuna sha'awa a kan faduwar ba kuma ya gaya wa ɗan wasan Barca ya tashi.

Barca ta yi canjin dan wasa

Ferran Torres da Joao Felix sun shiga cikin filin a kasa da rabin sa'a na buga wasa, yayin da suka maye gurbin Lewandowski da Raphinha.

Real Madrid ta kai wa Barcelona farmaki

Jude Bellingham ne ya saka wa Vinícius Júnior kwallo amma ya dan fadi.

Dan wasan na Brazil ya samu bugun daga gefe amma ya aika kwallon zuwa kusurwar dama ta sama.

Kati na biyu ga Real Madrid

An ba Ucas Vazquez katin gargadi saboda keta da ya yi wa Joao Cancelo.

Kokarin farko na Real Madrid baya hutu

Vinicius Junior ya mika kwallo ga Jude Bellingham, wanda ya juya ya buga ta ga ragar Barca daga wajen gida.

Sai dai ya mika kwallon kai tsaye a mai tsaron gida.

An dawo daga hutu: Real Madrid 1-1 Barcelona

Real za ta iya sanya hannu a kan kofin La Liga nan da mintuna 45 masu zuwa.

Barcelona ta yi canjin dan wasa bayan dawowa daga hutun rabin lokaci inda Fermín López ya maye gurbin Andreas Christensen da ya zura kwallo a raga.

Lamine Yamal ya yi kokarin bugun kafar hagu daga wajen gida amma ta je kai tsaye ga mai tsaron gidan Real Madrid.

Hutun rabin lokaci — Real Madrid 1-1 Barcelona

Real yakamata ta kasance kan gaba, saboda Barca tana farautar nasara kuma tana samun babban dama a yunkurin kutsawa gaba.

Frenkie de Jong ya ji rauni kafin a tafi hutun rabin lokaci kuma Pedri zai maye gurbinsa.

Wannan babbar koma baya ce amma kuma canji mai kyau, domin idan ana yin kwatancen Man City, De Jong na iya zama mafi kusanci ga Rodriyayin da Pedri ya fi kama da Bernardo Silva.

Hutun rabin lokaci — Real Madrid 1-1 Barcelona

Online view pixel