Ambaliya a Dubai Ta Halaka Dan Shekara 70, an Yi Mamakon Ruwan Sama

Ambaliya a Dubai Ta Halaka Dan Shekara 70, an Yi Mamakon Ruwan Sama

  • Ambaliyar ruwa ta mamaye birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa bayan samun ruwan sama na shekara guda cikin sa'o'i 12 kacal
  • A halin yanzu an rufe makarantu a fadin masarautar kuma ma'aikatan gwamnati galibi suna aiki daga gidajensu
  • UAE ta dakatar da saukar fasinja a filin jiragen sama na babbar tashar birnin daga karfe 8:00 na safe zuwa tsakar daren ranar Laraba, 17 ga Afrilu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Dubai, UAE - Manyan manyan tituna da filin jirgin sama na Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sun cika da ambaliya bayan saukar mamakon ruwan sama.

Ambaliyar ruwa ta mamaye Dubai bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya
Ambaliyar ruwa ta mamaye manyan tituna da filin jirgin saman Dubai, dattijo ya mutu. Hoto: @EhikhuenmenM
Asali: Twitter

An fara ruwan saman ne da yammacin ranar Litinin, 15 ga watan Afrilu kuma ruwan ya tsananta da misalin karfe 9 na safiyar ranar Talata har zuwa yinin ranar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun buɗe wa matafiya wuta, sun yi awon gaba da mutane da yawa a titin Abuja

Ambaliyar ruwan Dubai ta halaka tsoho

‘Yan sanda sun ce wani dattijo dan shekara 70 ya mutu a lokacin da ruwa ya tafi da motarsa ​​a Ras Al-Khaimah, masarautar arewacin kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Aljazeera, bayanan yanayi sun nuna cewa yashi da titunan Dubai sun nutse a ambaliyar ruwan mai zurfin mita 20 (inci 0.79).

'Yan sanda da jami'an agajin gaggawa sun yi rangadi a kan titunan Dubai da ambaliyar ta shafa, inda suke haskaka fitulun agaji a kan hanyoyin da duhu ya mamaye.

An rufe makarantu da filin jirgi a Dubai

Filin jirgin saman Dubai ya dakatar da saukar fasinjoji daga karfe 8 na safe zuwa tsakar daren ranar Laraba 17 ga Afrilu.

Ambaliyar ta mayar da hanyoyi zuwa koguna sannan kuma ruwan ya mamaye gidajen jama'a da wuraren kasuwanci, kamar yadda CNN ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Babban fasto ya hasasho matsalar da ke tunkarar Najeriya, ya aika da sakon gaggawa ga Tinubu

An rufe makarantu a cikin masarautu bakwai da ke a karkashin daular UAE kuma ma'aikatan gwamnati galibi suna aiki daga gidajensu.

Hukumomi sun soke bude makarantu kuma gwamnati ta sake ba ma'aikata damar yin aiki daga gida a ranar Laraba, 17 ga Afrilu sakamakon ambaliyar ruwa mai zurfin 145mm (inci 5.7) da ta mamaye birnin a ranar Talata, 16 ga Afrilu.

"Wahalar da ke tunkarar Najeriya" - Ayodele

A wani labarin daga nan gida Najeriya, malamin addinin Kirista, Primate Ayodele ya ce ya hango wahalar rayuwa da ke tunkarar kasar nan ma damar gwamnati ba ta dauki mataki ba.

Ayodele ya yi nuni da cewa Najeriya za ta kara fadawa cikin matsin tattalin arziki, kayan masarufi za su kara yin tsada, amma shugaban kasa Bola Tinubu zai iya hana hakan ta faru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel