Neman Kudi: “Mun Kashe Bafullatana Domin Yin Tsafi”, Malamin Tsibbu Ya Fallasa Abokansa

Neman Kudi: “Mun Kashe Bafullatana Domin Yin Tsafi”, Malamin Tsibbu Ya Fallasa Abokansa

  • An kama wani malamin tsibbu, Onifade Oyekanmi tare da abokansa guda uku bisa laifin kashe wata Bafullatana saboda yin tsafi
  • Onifade ya amsa cewa shi da abokansa sun shake Bafullatanar har lahira a gidansa da ke Ibadan a jihar Oyo saboda abin duniya
  • Bokan ya bayyana cewa ya gayyaci wada abin ya shafa, mai zaune a jihar Osun da ta zo gidansa a Ibadan inda a nan ne suka kashe ta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Osun – Wani malamin tsibbu a Ifa, Onifade Oyekanmi, ya amsa laifin hada baki da abokansa wajen kashe wata Bafulattana mai shekaru 45, Usman Aminat domin yin tsafin kudi a Ibadan, jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Tashin farashin Dala: Kokarin da CBN yake yi na daidaita Naira a kasuwar canji

Mummunan lamarin ya faru ne a gidan Onifade da ke Iyana Ajia a Ibadan a ranar 13 ga Maris, 2024.

Malamin tsibbu a Ifa ya hada baki da abokansa sun kashe Bafullata saboda neman kudi
‘Yan sanda sun cafke malamin tsibbu bayan samun rahoton wata Bafullatana ta bata. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Osun, SP Yemisi Opalola ne ya bayyana haka a yayin da ake gabatar da wadanda ake zargin a Osogbo a ranar Juma’a, 19 ga watan Afrilu, kamar yadda rahoton PM News ya nuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mun shake ta har lahira" - Onifade

Opalola ya ce an kama wadanda ake zargin ne bayan dan matar ya kai rahoton batan ta a ofishin ‘yan sanda na Apomu da ke Osun.

Onifade ya ce shi da abokansa sun shake ta har lahira bayan ya gayyace ta zuwa Ibadan daga gidanta da ke Apomu, jihar Osun.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, ya bayyana cewa an kona wasu sassan gabobinta tare da hanjin alade da akuya zuwa burbushi.

Kara karanta wannan

Malaman musulunci sun shiga gargadin DisCos a kan lalacewar wutar lantarki

Yadda aka kashe Bafullatana saboda tsafi

Malamin tsibbun tare da Oyebode Olalekan mai shekaru 40 da Ifayemi Ojeleke mai shekaru 32 da Jamiu Lasisi mai shekaru 40 ake zargin sun aikata laifin.

“Ni da abokaina ne muka shake ta har lahira. Daya daga cikinsu ya yi gunduwa da gabobinta inda muka yi amfani da wasu sassan jikinta. Mun kona hanjinta tare da na alade da hanjin akuya har suka koma gari.
"Mun so mu yi amfani da ita wajen yin tsafi domin neman kudi amma malamin addinin Musuluncin da ya gaya min lakanin bai ba ni umarnin yadda za a yi amfani da garin ba kafin a kama mu."

- Onifade Oyekanmi

An bankado nama mai guba a Kwara

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito yadda wata kungiya ta kai koke ga gwamnatin jihar Kwara kan wani naman shanu da ta yi zargin yana dauke da guba.

Kungiyar ta yi ikirarin cewa mahauta sun fara sayar da naman a kasuwar Mandate da ke Ilorin. Tuni dai gwamnatin jihar ta fara bincike kan lamarin tare da kwace naman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel