Abun Bakin Ciki
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tura sakon ta'azziyarsa bayan rasuwar mahaifiyar Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa da dansa a wannan mako.
Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindiga sun hallaka Rabaran Tobias Chukwujekwu Okonkwo a jihar Anambra bayan mummunan harin da aka kai masa a jiya Alhamis.
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, Clement Adesuyi Haastrup ya zama sabon sarki a masarautar Ijesa a matsayin Owa-Obokun bayan kada kuri'a kan nadin.
Tsohon kwamishinan yaɗa labarai da sadarwa na jihar Kwara, Alhaji Abdulrahim Adisa ya kwanta dama, ya rasu yana da shekaru 91 a duniya ranar Alhamis.
Soja ya kashe matashi Abdullahi Muhammad a kofar barikin Rukuba. Rundunar sojoji ta fara gudanar da bincike, tare da yin alkawarin adalci da hukunta mai laifin.
Hukumomi a Karamar Hukumar Garun Malam a jihar Kano sun rufe Kasuwar Tumatur ta Kwanar Gafan saboda zargin ayyukan fasadi, karuwanci da wasu munanan dabi'u.
Matar tsohon gwamnan Ondo, Betty Akeredolu ta yi kaca-kaca da Gwamna Lucky Aiyedatiwa kan shirin gudanar da taron tunawa da mijinta, Rotimi Akeredolu.
Masu garkuwa da mutane sun kashe wani yaro dan shekara 10 Tasi’u Abdullahi a Filato duk da karbar kudin fansa. An rahoto cewa an gano gawarsa ne a cikin buhu.
Barayi sun haura katanga, sun sace akuyar Kirsimet a Gwagwalada da ke Abuja. Mai akuyar ya kai rahoto yayin da ‘yan sanda suka soma bincike don gano barayin akuyar.
Abun Bakin Ciki
Samu kari