Ana Murna Dangote Ya Fara Fitar Da Mai, Sojoji Sun Tafka Ta'asa a Matatar, an Dauki Mataki

Ana Murna Dangote Ya Fara Fitar Da Mai, Sojoji Sun Tafka Ta'asa a Matatar, an Dauki Mataki

  • Sojojin Najeriya sun yi Allah wadai da wasu jami'anta biyu da aka kama da zargin sata a matatar Aliko Dangote
  • Rundunar ta tabbatar da cafke jami'an nata biyu inda ta ce yanzu haka ana kan bincike kuma za su fuskanci hukunci
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran hukumar, Onyema Nwachukwu ya fitar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Rundunar sojojin Nigeriya ta ba da umarnin tsare wasu jami'anta guda biyu kan zargin sata.

Rundunar ta ba da umarnin ne bayan kama sojojin da zargin yin sata a matatar man Aliko Dangote da ke Legas.

An cafke wasu sojoji da zargin tafka barna a matatar man Dangote
Rundunar sojoji ta garkame jami'anta 2 kan zargin sata a matatar Aliko Dangote. Hoto: @HQNigerianArmy, @DangoteGroup.
Asali: Twitter

Wane mataki sojojin suka dauka?

Kara karanta wannan

Rundunar sojin Najeriya za ta ginawa sojoji gidaje bayan ritaya daga aiki

Hukumar ta tabbatar da cewa tana gudanar da bincike inda ta ce da zarar ta kammala kuma ta same su da laifi za su fuskanci hukunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daraktan yada labarai na rundunar, Onyema Nwachukwu shi ya bayyana haka a wata sanarwa a shafin Facebook a jiya Laraba 17 ga watan Afrilu.

Onyema ya ce rundunar ta kaɗu da samun labarin zargin sata kan wasu jami'anta a matatar Dangote da ke Legas.

Jami'in ya ce wannan abin takaici ne duk da kokarin kare faruwar hakan da 'yan sa-kai da jami'an tsaron matatar suka yi.

Martanin sojoji kan sata a matatar Dangote

"Rundunar sojoji ta kaɗu da samun jami'anta ds zargin sata a matatar Dangote da ke Legas."
"Wannan laifi da suka aikata wanda jami'an tsaron matatar suka yi kokarin dakilewa abin takaici ne kuma ba koyarwar rundunar ba ce."

Kara karanta wannan

EFCC za ta gurfanar da shahararren dan kasuwa Cubana bisa zargin cin zarafin Naira

"Wadanda ake zargin an kama su, kuma suna garkame inda ake ci gaba da bincike kan lamarin."

- Onyema Nwachukwu

Rundunar ta ce wani ɗan kwangila ne mai suna Mista Smart ya dauki nauyinsu inda ya musu karya ya manta wasu manyan wayoyin wutar lantarki a matatar.

Sojoji sun ƙaryata kisan mutane a Filato

A wani labarin, kun ji cewa rundunar sojojin Nigeriya sun yi martani kan zargin kisan wasu mutane a jihar Filato.

Rundunar ta ƙaryata zargin da wasu kungiyoyi suka yi da cewa jami'anta sun hallaka mutane da dama da wasu 'yan sa-kai.

Kungiyoyin sun zargi rundunar da bindige mutanen ne musamman 'yan sa-kai da ke kokarin kawo ɗauki a harin da aka kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel