Ana Jimamin Rasuwar Tsohon Dan Majalisar Tarayya a Kwara, Sanata Ya Tafka Babban Rashi

Ana Jimamin Rasuwar Tsohon Dan Majalisar Tarayya a Kwara, Sanata Ya Tafka Babban Rashi

  • Ana jikin jimamin rasuwar Sanata Ibrahim Rafiu a jihar Kwara, an sanar da mutuwar wani dattijo a jihar a yau Laraba 17 ga watan Afrilu
  • Marigayin Alhaji Suleiman Omar shi ne mahaifin Sanata da ke wakiltar Kwara ta Arewa, Sadiq Umar a Majalisar Dattawan Najeriya
  • Marigayin wanda tsohon sakatare ne a hukumar alhazan jihar ya rasu ne a daren jiya Talata 16 ga watan Afrilu da shekaru 86 a duniya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kwara - Mahaifin sanatan da ke wakiltar Kwara ta Arewa, Sadiq Umar ya riga mu gidan gaskiya a jihar.

Marigayin mai suna Alhaji Suleiman Omar ya rasu ne a daren jiya Talata 16 ga watan Afrilu a jihar Kwara.

Kara karanta wannan

Jimami yayin da tsohon Sanata Ibrahim ya riga mu gidan gaskiya, bayanai sun fito

Sanata a jihar Kwara ya tafka babban rashi
Mahaifin Sanata Sadiq Umar ya rasu a jihar Kwara da shekaru 86. Hoto: Sadiq Umar.
Asali: Facebook

Wani mukami marigayin ya riƙe a Kwara?

Dattijon wanda ya rasu da shekaru 86 a duniya ya taɓa riƙe muƙamin sakataren Hukumar alhazai a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, ya shafe shekaru 35 ya na aikin gwamnati wanda ya ba da gudunmawa sosai a gwamnati.

Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazak ya nuna alhini kan rasuwar dattijon a jihar.

Gwamnan kwara ya tura sakon ta'aziyya

Gwamnan ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin da kuma Sanata Sadiq Umar kan wannan babban rashin da suka yi.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Rafiu Ajakaye ya fitar a yau Laraba 17 ga watan Afrilu a shafin Facebook.

Sanarwar ta bukaci sanatan da iyalansa da su godewa Ubangiji kan irin gudunmawar da mahaifinsu ya bayar a rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Katsina: Gwamna Dikko Radda ya yi muhimmin nadi a gwamnatinsa

Ya yi addu'ar ubangiji ya jikansa ya kuma tabbatar da shi a gidan aljanna firdausi madaukakiya.

Tsohon sanatan Kwara ya rasu

A wani labarin mai kama da wannan, kun ji cewa tsohon sanata a jihar Kwara, Ibrahim Rafiu ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin Sanata Rafiu ya rasu ne a yau Laraba 17 ga watan Afrilu ya na da shekaru 57 a duniya.

Iyalan marigayin ne suka tabbatar da rasuwar Sanata Ibrahim a wata sanarwa da suka fitar a yau Laraba 17 ga watan Afrilu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel