Kwara: Gwamnati Ta Fara Bincike Kan Zargin Ana Sayar da Naman Shanu Mai Guba

Kwara: Gwamnati Ta Fara Bincike Kan Zargin Ana Sayar da Naman Shanu Mai Guba

  • Gwamnatin Kwara ta kwace naman akalla shanu 33 a kasuwar Mandate da ke Ilorin domin gudaar da bincike kan zargin yana da guba
  • Wata kungiya mai suna 'Kwara Monitoring Group (KMG)' ta mika koke ga gwamnatin jihar kan cewa mahauta na sayar da naman mai guba
  • Gwamnati tana kira ga jama’a da su kwantar da hankula yayin da tawagar ta ke bincike domin gano gaskiyar wannan ikirarin na kungiyar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ilorin, jihar Kwara - Gwamnatin jihar Kwara ta yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu kan zargin ana sayar da nama mai guba a kasuwar Mandate, Ilorin babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Mulkin Tinubu ya dara shekaru 16 a PDP ta fuskar tsaro, Hadimin Tinubu

Gwamnatin Kwara ta magantu kan nama mai guba da ake fargabar ana sayarwa
Kwara: Gwamnati ta kwace dukkanin naman shanun da ake zargin suna dauke da guba a kasuwar Ilorin. Hoto: @followKWSG
Asali: Twitter

Rokon na gwamnatin ya biyo bayan rahoton mutuwar shanu 33 sakamakon guba da ake zargin kuma an fara sayar da naman su, in ji rahoton jaridar The Punch.

"Guba ta kashe shanu 33" - KMG

Wata kungiya mai suna 'Kwara Monitoring Group (KMG)' a cikin wata sanarwa da ba a sanyawa hannu ba a ranar Lahadi, 21 ga Afrilu, 2024, ta ankarar da gwamnati kan lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

KMG ta ja bukaci kwamishinonin muhalli da lafiya da kuma hukumar kare muhalli ta jihar Kwara da su dauki matakin gaggawa don hana naman mai guba ya je hannun jama'a.

Kungiyar ta ce:

“Sama da shanu 33 ne ake zargin sun sha guba kuma sun mutu, amma abin mamaki sai aka yanka matattun dabbobin aka raba ga mahauta domin a sayar da su.
“Abin ya faru ne a kan titin Atere (wanda ke kan hanyar zuwa matsugunnin dalibai na Al Hikma) a cikin Kwalejin Larabci da Ilimin Islama, a Ilorin.

Kara karanta wannan

Tuhumar rashawa: Shari'ar gwamnatin Kano da Abdullahi Ganduje ta gamu da cikas

Gwamnatin Kwara ta fara bincike

Sai dai sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar a shafinta na Twitter ta nuna cewa tawagar gwamnatin jihar Kwara sun isa kasuwar Mandate inda suka kwace naman shanun da ake zargin yana da guba.

Sanarwar ta samu sa hannun hadin gwiwa na kwamishinonin lafiya da aikin gona, Dr Amina El-Imam da Toyosi Thomas Adebayo.

Sanarwar ta kara da cewa:

"Gwamnati ta kwace dukkanin naman da ake zargi tare kai shi dakin gwaje-gwaje domin gano gaskiya kan wannan zargi da kuma duba bayanan masu ruwa da tsaki na kasuwar Mandate.
“Gwamnati tana kira ga jama’a da su kwantar da hankula yayin da tawagar ta ke bincike domin gano gaskiyar jita-jitar cewa naman na da guba."

Dakatar da Ganduje: APC ta yi martani

A wani labarin, jam'iyyar APC a jihar Kano ta kuma yin martani bayan da wasu da suka yi ikirarin su shugabannin jam'iyyar ne na gunduma suka dakatar da Abdullahi Ganduje.

Legit Hausa ta ruwaito jam'iyyar a matakin jihar ta yi fatali da wannan dakatarwar tare da cewa aikin 'yan taware ne kuma za ta warware bakin zaren nan ba da dadewa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel