InnalilLahi: An Shiga Ɗimuwa Bayan 'Yan Bindiga Sun Hallaka Fitaccen Basarake a Taraba

InnalilLahi: An Shiga Ɗimuwa Bayan 'Yan Bindiga Sun Hallaka Fitaccen Basarake a Taraba

  • An shiga wani irin yanayi bayan wasu 'yan bindiga sun hallaka wani basarake, Abdulmutalib Nuhu a jihar Taraba
  • Maharan sun kai farmakin ne a daren jiya Alhamis 18 ga watan Afrilu inda suka hallaka basaraken a cikin fadarsa
  • Legit Hausa ta tattauna da wani mazaunin yankin inda ya koka kan kisan gillar da aka yi wa basaraken a daren jiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Taraba - Wasu 'yan bindiga sun yi ajalin wani fitaccen basarake a jihar Taraba bayan kai mummunan farmaki.

Maharan sun bindige Abdulmutalib Nuhu da ke sarautar kauyen Sansani a karamar hukumar Gasol a jihar, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

"Lamarin ya yi muni" Ƴan bindiga sun kewaye gari guda, sun tafka mummunar ɓarna a Kaduna

Yan bindiga sun yi ajalin babban basarake a Taraba
Wasu 'yan bindiga sun hallaka nasara a jihar Taraba. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Facebook

Yaushe aka kai harin a Taraba?

Lamarin ya faru ne a daren jiya Alhamis 19 ga watan Afrilu a yankin awanni kadan kafin gudanar da kasaitaccen bikin gargajiya a karamar hukumar Ibbi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindigan sun durfafi kauyen Sansani da misalin karfe 9:00 na dare inda suka wuce kai tsaye fadar Sarkin tare da hallaka shi, cewar Politics Nigeria.

Yayan marigayin mai suna, Nuhu Sansani ya ce maharan sun kawo farmakin ne da dare inda suka hallaka basaraken tare da tafiya da wayoyinsa, cewar Daily Trust.

Yadda maharan suka hallaka basaraken

"Su iso kauyen da misalin karfe 9:00 na dare inda suka wuce kai tsaye fadar suka hallaka shi tare da ɗauke wayoyinsa guda biyu."
"Yayin da suke ficewa daga kauyen, sun ci karo da wani akan babur inda suka harbe shi har ya karye a kafa sannan suka yi tafiyarsu."

Kara karanta wannan

Sojoji sun bindige 'yan sakai da fararen hula yayin harin Filato? Gaskiya ta fito

- Nuhu Sansani

'Yan sanda ba su ce komai ba tukuna

Mukaddashin kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, ASP James Lashen ya ce ya na kan hanyar zuwa ofishinsu ba shi da labarin harin 'yan bindigan.

"Ba ni da masaniya, ina kan hanyar zuwa ofis, idan na samu wani karin bayani zan sanar da ku."

- James Lashen

Martanin wani mazaunin yankin

Legit Hausa ta tattauna da wani mazaunin yankin inda ya koka kan kisan gillar da aka yi wa basaraken.

Kamaludden Bala Wakili ya ce an yi sallar Isha lafiya da basaraken inda ya yi sallama ga jama'a ya koma.

Kawai sai aka ga wasu miyagu sun rurrufe fuskokinsu da bakin kyalle inda suka shiga gidansa tare da bindige shi.

"Wannan bawan Allah kusan mai gida ya ke a gare mu, an yi sallar Isha da shi lafiya ya tafi gida.
"Wasu azzalumai sun yi masa kisan gilla sun rurrufe fuskokinsu, fitarsu ke da wuya matansa suka fito suna ihu an harbe shi wanda kafin a ankara rai ya yi halinsa."

Kara karanta wannan

Halin kunci: Matasa sun sake kai hari kan motocin kayan abincin tallafi, sun tafka barna

- Kamaludden Bala Wakili

Kamaludden ya ce za a jana'izarsa bayan sallar Juma'a inda ya ce 'yan yankin suna cikin tashin hankali ganin cewa sarakuna ma ba su tsira ba bare talakawa da ba su da masu gadinsu.

'Yan mata sun mutu yayin hatsarin jirgi

A wani labarin, kun ji cewa wasu 'yan mata uku sun rasa rayuwarsu yayin hatsarin jirgin ruwa a jihar Neja.

Lamarin ya faru yayin da 'yan matan suka kife a cikin kogi a kan hanyarsu ta zuwa gaisuwar sallah a karshen mako.

Asali: Legit.ng

Online view pixel