Sanata mai wakiltar babban birnin tarayya Abuja a majalisar dattawa, Ireti Kingibe, ta shirya komawa jam'iyyar ADC. Ta sanya lokacin da za ta yi rajista.
Sanata mai wakiltar babban birnin tarayya Abuja a majalisar dattawa, Ireti Kingibe, ta shirya komawa jam'iyyar ADC. Ta sanya lokacin da za ta yi rajista.
Gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da nadin dan uwan Abubakar Malami (SAN) a matsayin shugaban hukumar KEBGIS bayan ya sauya sheka zuwa APC mai mulki.
Magoya bayan APC sun gudanar da zanga-zanga, sun caccaki Abdullahi Ganduje. Ana zargin Gwamnatin Kano da saida rajistar APC ga Bola Tinubu da jawo bakin-jini.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi watsi da fastocin yakin neman zaben shugaban kasa da suka hada shi da tsohon gwamnan CBN, Charles Soludo.
Samuel Ortom ya fadi abin da ya sa wasu Gwamnonin PDP ke sauya-sheka. Gwamnan Benuwai ya ce abokan aikinsa na komawa APC ne saboda EFCC na iya kama su a 2023.
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya roki gwamnatin tarayya da ta janye dakatar da ayyukan Twitter a Najeriya domin a cewarsa manhajar na da matukar tasiri.
Adamu Muhammad Bulkachuwa ya ce idan akwai mai ganin cinta a Kudu ko a Arewa, ya tsaya takaran 2023. Da wannan ra’ayi na Bulkachuwa, Arewa za ta iya zarcewa.
Tunde Bakare yana ganin tsofaffin da ke mulki a yau suka fara kashe Najeriya a baya. Bakare ya na ganinn zama da Muhammadu Buhari, da shi da babu duk daya.
Wani tsohon dan takarar shugaban kasa da ya sha kaye a hannun shugaba Buhari ya caccaki Twitter saboda goge rubutun da shugaban ya yi na daukar mataki kan wasu.
Abdurrahman Kawu Sumaila, wani tsohon hadimin Buhari ya bayyana dalilan da za su sa duk dan Najeriya mai tunani da hankali ya ki zaben dan kudu maso gabas.
Bangaren Abdulaziz Yari sun yi zugum game da sauya-shekar Gwamnan jihar Zamfara. Tsohon Gwamna Yari, ya na sauraron shigowar Gwamna Matawalle Jam’iyyar APC.
Siyasa
Samu kari