Siyasa: Tsohon Gwamna Yari, ya na kawowa APC cikas wajen karbar Gwamna daga PDP

Siyasa: Tsohon Gwamna Yari, ya na kawowa APC cikas wajen karbar Gwamna daga PDP

- Akwai yiwuwar Gwamna Bello Matawalle ya shiga jam’iyyar APC a watan nan

- Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa Gwamnan ya na ta shirin ficewa daga PDP

- Ana zargin bangaren Abdulaziz Yari ne su ka sa har yanzu bai sauya-shekar ba

Rahotanni daga jaridar Daily Trust suna kara tabbatar da cewa Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya kammala shirin ficewa daga jam’iyyar PDP.

Majiyar ta bayyana cewa Bello Matawalle zai sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC a kwanan nan. Da aka jefa masa wannan tambaya, sai yace ya na yin nazari.

Ana tunanin daga cikin shirye-shiryen ne gwamna Bello Matawalle ya sauke duka hadimai, da mukarrabai, da kwamishinonin jihar Zamfara a ranar Talata.

KU KARANTA: Bello Matawalle yana neman sauya-sheka daga PDP zuwa APC

Bello Matawalle ya karkare yadda zai fice daga jam’iyyar PDP data taimaka masa wajen zama gwamna, amma yana fuskantar cikas a wajen komawa APC.

Bangaren tsohon gwamna, Abdulaziz Yari, wanda suke rike da shugabancin jam’iyyar APC sun zamewa gwamna mai-ci ala-kai-kai wajen shirin sauya-sheka.

Tun da kwamitin Mai Mala Buni ya sulhunta Abdulaziz Yari da abokin fadarsa, Sanata Kabiru Marafa, aka shiga lissafin yadda za a tunkari zabe mai zuwa.

Yayin da wasu manyan APC ke kokarin jawo Matawalle zuwa jam’iyyar mai mulki, ana zargin cewa Abdulaziz Yari da mutanensa ba su goyon-bayan haka.

KU KARANTA: Matawalle ya tsige Mukarrabai, ya ce su mika kayan Gwamnati

Siyasa: Tsohon Gwamna Yari, ya na kawowa APC cikas wajen karbar Gwamna daga PDP
Gwamna Bello Matawalle Hoto: @Bellomatawalle1
Asali: Twitter

Wata majiyar ta bayyana cewa Abdulaziz Yari ba ya goyon-bayan magajinsa ya dawo APC ne saboda ba a tuntube shi a lokacin da aka fara dauko maganar ba.

Mai magana da yawun tsohon gwamnan, Alhaji Ibrahim Birnin Magaji, ya ce ko kadan wannan rade-radi da ke yawo ba ya damunsu, ko ya tada masu hankali.

Wani daga cikin kwamishonin da aka sallama ya tabbatar da wannan shiri a kasa. Bayan an ji cewa gwamnan ya zauna da ‘yan majalisan Zamfara a kan hakan.

Idan har Matawalle ya yi nasarar sauya-sheka zuwa APC, zai zama gwamna na uku da jam’iyyar PDP ta rasa a shekaru biyu, kuma jiha ta hudu da APC ta karbe.

A watan da ya gabata ne gwamnan Kuros Riba, Ben Ayade ya bar PDP ya koma APC. Kafin nan gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya sauya-sheka zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel