Ya kamata Twitter ta bar Najeriya: Adamu Garba ya caccaki Twitter saboda Buhari

Ya kamata Twitter ta bar Najeriya: Adamu Garba ya caccaki Twitter saboda Buhari

- Tsohon dan takarar shugaban kasa Adamu Garba ya caccaki kamfanin Twitter bisa goge rubutun shugaba Buhari

- Ya yi ikirarin cewa, bai kamata kamfanin Twitter ya shiga lamurran siyasar cikin gida ta Najeriya ba ko kadan

- Ya kuma yi kira ga kamfanin da ya tattara nashi ya nashi ya bar Najeriya saboda shiga hurumin da ba nashi ba

Adamu Garba, wani tsohon dan takarar shugaban kasa a Najeriya ya caccaki kamfanin Twitter bisa goge jawabin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kan masu kokarin kifar da gwamnatinsa.

A makon nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jawabi ta shafin Twitter cewa, duk masu kokarin kitsa kifar da gwamnatinsa su shirya za su shiga firgici, kuma zai musu magana da yaren da suka fi fahimta, amma kamfanin ya goge rubutun.

A wani rubuta da wakilin Legit.ng Hausa ya gani daga shafin Adamu Garba, ya gano inda matashin kuma tsohon dan takarar shugaban kasa ke caccakar shawarar da Twitter ta yanke na goge rubutun, yana mai kira ga tattarawar Twitter ta bar Najeriya.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Hukumar Jarrabawar NECO Ta Nada Sabon Shugaban Riko

Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa Adamu Garba Ya Caccaki Twitter Kan Goge Jawabin Buhari
Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa Adamu Garba Ya Caccaki Twitter Kan Goge Jawabin Buhari Hoto: ripplesnigeria.com
Asali: UGC

A kalamansa, cewa ya yi:

"Twitter ba shi da 'yancin shiga cikin harkokin siyasarmu na gida. Kamfani ne ba gwamnati ba.
"Ta hanyar cire jawabin shugaban kasar muka zaba ta hanyar dimokiradiyya ga mutanen Najeriya, Twitter na bukatar tattara na-ya-nata ta bar Najeriya.
"Ya kamata Twitter ya fita daga Najeriya."

Lamurran tsaro na ci gaba da karuwa a Najeriya, musamman a yankunan kudu maso gabas, wannan yasa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jawabin da ya jawo cece-kuce.

A yankunan kudu maso gabas, an barnata kadarorin gwamnati tare da hallaka jami'an tsaro da dama, lamarin da ya jawo firgici tsakanin mazauna da bakin da ke zuwa yankin.

KU KARANTA: Ni Zan Rera Wakar Taken Kasa Idan Aka Sauyawa Najeriya Suna, Inji Naira Marley

A wani labarin, Wani tsohon hadimin Shugaba Buhari, kan lamuran Majalisa, Abdurrahman Sumaila, ya ce ‘yan Najeriya masu tunani ba za su jefa rayukansu cikin hadari ba don mara wa takarar duk wani dan siyasar Kudu maso Gabas da ke neman shugabancin kasar nan a 2023 ba.

Sumaila ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kano ranar Alhamis, jaridar Punch ta ruwaito.

“Tare da wadannan munanan dabi’un da mutanen Kudu-maso-Gabas suka aikata, ta yaya 'yan Najeriya za su ba su amanar su shugabance mu?

Asali: Legit.ng

Online view pixel