‘Yan Buhariyya sun yi zanga-zanga a Hedikwatar APC, sun ce Ganduje ya saidawa Tinubu Jam'iyya

‘Yan Buhariyya sun yi zanga-zanga a Hedikwatar APC, sun ce Ganduje ya saidawa Tinubu Jam'iyya

- ‘Yan kungiyar BSO sun soki aikin rajistar Jam’iyyar APC da aka yi a Kano

- Buhari Support Organisation ta kai wa Shugabannin jam’iyya korafi a Abuja

- Ana zargin Gwamnatin jihar Kano da saida rajistar APC ga su Bola Tinubu

Wasu daga cikin ‘yan kungiyar Buhari Support Organisation watau BSO, sun shirya zanga-zanga, suna zargin shugabannin APC da rashin adalci a Kano.

Jaridar Daily Trust ta ce wadannan magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari sun ce ba ayi adalci wajen aikin rajistar ‘ya ‘yan jam’iyyar APC ba.

Wadanda suka yi wannan zanga-zanga sun dura hedikwatar jam’iyyar APC da ke garin Abuja, suka gabatar da korafinsu gaban shugabannin jam’iyya.

KU KARANTA: 2023: Ban fito da hotunan neman takara ba - Atiku

Kamar yadda Allafrica ta fitar da rahoto dazu, shugaban BSO na jihar Kano, Alhaji Shehu Dalhatu ya rubuta wannan korafi a ranar 7 ga watan Yuni, 2021.

Shehu Dalhatu ya bayyana cewa ba ayi wa ‘ya ‘yan jam’iyyar APC a jihar Kano rajista kamar yadda shugabannin jam’iyya suka tsara dokokin rajistar ba.

Korafin da ‘yan kungiyar BSO suka gabatar ya zargi kusoshin jihar Kano da nuna son kai, nuna wariya, da kitsa yadda za a ragewa APC farin jini a 2023.

Dalhatu a madadin BSO ya sanar da shugaba Muhammadu Buhari, mataimakinsa, Yemi Osinbajo, da shugaban rikon kwarya, Mai Mala Buni, abin da ya faru.

‘Yan Buhariyya sun yi zanga-zanga a Hedikwatar APC, sun ce Ganduje ya saidawa Tinubu Jam'iyya
‘Yan BSO na jihar Kano Hoto: Legit
Asali: Original

KU KARANTA: Dalilinmu na kai Ma’aikatan Kano makaranta su zama malamai - Kwamishina

“An sauke kwamitin rajistar ne a gidan gwamnati, aka bar aikin yi wa mutanen gundumomi 484, da kananan hukumomi 44 a karkashin jami’an gwamnati.”

Masu zanga-zangar sun zargi jagororin APC da aka tura zuwa Kano da yin abin zai bata sunan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya jawo APC bakin-jini.

Daga cikin wadanda aka ki yi wa rajistar zama ‘dan APC, har da wani tsohon ‘dan majalisa kuma hadimin shugaban kasa, suka ce an saidawa Bola Tinubu rajistar.

Yayin da ake maganar siyasar APC, dazu kun ji labari cewa ana zargin Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya na kutun-kutun domin ya karbi rikon uwar Jam’iyya.

Mai Mala Buni shi ne shugaban rikon kwarya, ya rike Sakataren jam’iyyar APC a baya. Ana tunanin zai ajiye kujerar gwamna, ya zama shugaban APC na kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel