Gwamnan Najeriya Ya Aika Sako Ga Buhari, Ya Bayyana Dalilai 5 Da Zai Sa A Janye Dakatarwar Da Aka Yiwa Twitter

Gwamnan Najeriya Ya Aika Sako Ga Buhari, Ya Bayyana Dalilai 5 Da Zai Sa A Janye Dakatarwar Da Aka Yiwa Twitter

- Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya nemi gwamnatin tarayya da ta janye dakatarwar da ta yiwa Twitter

- Seyi Makinde ya ce dandamalin na da matukar alfanu musamman ga al'umman kasar

- Ya ce shafin sada zumunta ya zama hanyar samun abinci ga 'yan Najeriya da dama

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya roki gwamnatin tarayya da ta janye dakatar da ayyukan Twitter a Najeriya.

Makinde, wanda shi ne shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kudu maso yamma, ya yi rokon ne a cikin wata sanarwa ta shafin Instagram a ranar Asabar, 5 ga watan Yuni.

Dan siyasan, wanda ya ce bai kamata shugabanni su dunga daukar mataki na bacin rai kan batutuwa ba, ya yi iƙirarin cewa shafin yanar gizon yana da fa'idodi masu yawa ga ƙasar.

KU KARANTA KUMA: Bidiyon ruwan kudi da aka yi yayin da wani matashi yayi shigar kasaita a wajen bikin zagayowar haihuwarsa

Gwamnan Najeriya Ya Aika Sako Ga Buhari, Ya Bayyana Dalilai 5 Da Zai Sa A Janye Dakatarwar Da Aka Yiwa Twitter
Gwamnan Najeriya Ya Aika Sako Ga Buhari, Ya Bayyana Dalilai 5 Da Zai Sa A Janye Dakatarwar Da Aka Yiwa Twitter Hoto: Seyi Makinde
Asali: Twitter

Ya yi gargadin cewa haramcin zai shafi kimar kasa da kasa ta fuskar zamantakewa da tattalin arziki.

Makinde ya lissafa wasu kyawawan amfanin Twitter a kasar da suka hada da:

1. Gwamnan ya bayyana cewa Twitter ya zama dandalin matasa kuma hakika dukkan yan Najeriya suna amfani da shi wajen sauke hakkin su na bayyanawa da kuma wallafa ra'ayi.

KU KARANTA KUMA: Haramta Twitter: FG ta bayyana dalilai 3 da suka sa aka dakatar da kafar sadarwar

2. Shugaban na PDP ya nuna cewa ‘yan Najeriya suna amfani da dandamali wajen yin korafi, jayayya da ba da martani ga gwamnati da hukumominta wadanda su kuma suke amfani da wadannan don inganta manufofi.

3. Ya bayyana cewa shafin sada zumuntar ya zama hanyar samun abinci ga 'yan Najeriya da dama.

4. Makinde ya kuma lura cewa kungiyoyin sadarwar zamani suna samun kudin shiga daga amfani da dandalin wajen sanya sakonnin sadarwa a madadin abokan huldar su.

5. Gwamnan ya ci gaba da bayanin cewa kasuwancin da basu da shagunan zahiri sun dogara ne da kamfanin Twitter wajen tallata hajojin su da ayyukansu.

Wasu manyan yan Naeriya sun soki dakatar da Twitter

Kafafen sada zumunta sun cika da cece-kuce biyo bayan umarnin gwamnatin Buhari na dakatar da ayyukan Twitter a fadin kasar saboda goge rubutun shugaban kasa da Twitter din ta yi.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar da kuma tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya Abubakar Bukola Saraki, sun tofa albarkacin bakinsu kan umarnin na gwamnatin Buhari.

A wasu rubutun da Legit.ng Hausa ta gano na jiga-jigan 'yan siyasan, ta gano inda suke martani kan batun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel