A shirye nake da na mutu domin Najeriya: muhimman batutuwa 9 da Buhari ya gabatar a jawabin ranar Demokradiyya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a safiyar ranar Asabar, 12 ga watan Yuni, ya yi jawabi ga ‘yan Najeriya a ranar bikin dimokiradiyya ta bana, inda ya yi karin haske kan wasu muhimman ayyukan gwamnatoci da kalubalen tsaro da sauransu.
Anan Legit.ng ta lissafa muhimman abubuwa 10 daga jawabin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kasa:
KU KARANTA KUMA: Muhimman abubuwa 7 da shugaba Buhari ya fada yayin wata hira a ranar 11 ga Yuni
1. A shirye na ke in sadaukar da raina domin Najeriya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Asabar ya sha alwashin kare wanzuwar Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa sannan kuma ya yi wasici da zaben gaskiya da adalci a 2023.
Ya ce:
“Ranar da na shiga rundunaar Sojan Najeriya na shirya sadaukar da raina saboda Najeriya. A matsayina na shugabanku, na ci gaba da jajircewa wajan kare wanzuwar Najeriya."
2. Nan ba da jimawa ba dimokuradiyyar Najeriya za ta yi karfi
Shugaba Buhari ya ce dimokuradiyyar Najeriya za ta kasance a hanyar ci gaba a koyaushe da nufin isa ga balagaggiyar dimokradiyya, mai karfi, ci gaba kuma hadaddiyar kasa da za a lissafa ta a duniya.
3. Mun shawo kan wasu kalubale a cikin shekaru 2
Ya bayyana cewa a cikin shekaru biyu da suka gabata, Najeriya ta shaida kuma ta shawo kan yawancin kalubale wanda ka iya rusa sauran kasashe musamman wanda suka shafi tsaronmu baki daya.
KU KARANTA KUMA: Kimanin ‘Yan Nijeriya Miliyan 10.5m muka tsamo Daga Talauci Cikin Shekaru 2 - Shugaba Buhari
4. Nan ba da dadewa ba gwamnatina za ta kawo karshen matsalar rashin tsaro a Najeriya
Shugaban kasar ya lura cewa duk wani abin da ya faru, duk da kankantar lamarin yana sa shi damuwa matuka, ya kara da cewa nan take ya umarci hukumomin tsaro da su hanzarta amma su kubutar da wadanda lamarin ya cika da su sannan kuma a gurfanar da masu laifin a gaban kuliya.
5. Wasu masu laifi na amfani da mawuyacin halin da ake ciki a Najeriya
Buhari ya bayyana cewa abin takaici ne, kamar yadda a yawancin lokutan da ake rikici wasu miyagun yan Najeriya kan yi amfani da mawuyacin halin sannan suna samun riba daga hakan tare da kuskuren cewa bin ka'idojin dimokiradiyya ya kawo cikas ga gwamnatinsa ta hanyar magance su gaba daya.
6. Ba da daɗewa ba za mu kamo masu laifi da ke aikata munanan abubuwa a Najeriya
Ya ce tuni gwamnatinsa take magance matsalolin kuma nan ba da jimawa ba za ta gurfanar da wasu daga cikin wadannan masu laifin a gaban kuliya.
7. Zan kara sa hannun jari a harkar Noma
Shugaban kasar ya kuma ce ayyukan da gwamnati da Babban Bankin Najeriya (CBN) ke jagoranta na haifar da bunkasar tattalin arziki a cikin shekaru 6 da suka gabata an fi mayar da hankali ne ga bangaren noma, aiyuka, kayayyakin more rayuwa, wutar lantarki da kuma bangaren kiwon lafiya na tattalin arzikin kasar.
8. Zan fitar da talakawan Najeriya miliyan 100 daga talauci
Buhari ya kuma lura cewa an aiwatar da hangen nesansa na fitar da talakawan Najeriya daga talauci cikin shekaru 10, ya kara da cewa ana iya ganin hakan a cikin shirin tallafi na kasa.
9. Mun cimma nasarori matuka kan bunkasa ababen more rayuwa
Shugaban kasar ya kuma bayyana cewa shirin gwamnatinsa na kawo sauyi a baben more rayuwa na ci gaba tare da muhimman ayyukan cimma nasarori masu mahimmanci a karkashin Asusun Bunkasa ababen more rayuwa na Shugaban kasa; Gadar Neja ta biyu, Babban titin Legas zuwa Ibadan da kuma babbar hanyar Abuja-Kaduna-Zariya-Kano.
A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 10 ga watan Yuni, ya bayyana cewa makiyaya a Najeriya basa daukar komai sama da sanduna da adda don tara ciyawar shanun su.
Jaridar Guardian ta ruwaito cewa shugaban a tattaunawarsa da 'yan jaridu a yayin wata hira da gidan talabijin na Arise TV ya dage cewa makiyaya 'yan asalin Najeriya basa amfani da manyan makamai kamar AK-47.
Da yake ci gaba da magana, shugaban na Najeriya ya bayyana makiyayan da ke dauke da muggan makamai cewa ba 'yan Najeriya bane, tabbas daga wasu kasashen suke.
Asali: Legit.ng