Wani Kwamishina Ya Rasa Muƙaminsa Saboda Yaƙi Bin Gwamna Zuwa APC

Wani Kwamishina Ya Rasa Muƙaminsa Saboda Yaƙi Bin Gwamna Zuwa APC

- Gwamna Ben Ayade na jihar Cross Rivers ya sake sallamar wani kwamishinansa daga muƙaminsa

- Wannan na zuwa ne mako ɗaya bayan gwamnan ya sallami wasu kwamishinoninsa hudu saboda sun ƙi bin shi zuwa APC

- Rikicin siyasa na ƙara tsamari a jihar Cross Rivers tun bayan sauya sheƙar gwamnan jihar, Ayade, zuwa APC

Mako ɗaya da gwamnan jihar Cross Rivers, Ben Ayade, ya sallami kwamishinoninsa huɗu daga muƙamansu saboda sun ki binsa zuwa sabuwar jam'iyyar sa, gwamnan ya sake sallamar wani, kamar yadda punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Sunayen Wasu Makusantan Shugaba Buhari da Suka Bijire Wa Umarninsa Na Hana Amfani da Twitter

Gwamna Ben Ayade ya sake sallamar kwamishinan ayyuka na musamman daga muƙaminsa, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KwamIshina Ya Rasa Muƙaminsa Saboda Yaƙi Bin Gwamna Zuwa APC
KwamIshina Ya Rasa Muƙaminsa Saboda Yaƙi Bin Gwamna Zuwa APC Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Gwamna Ayade a ranar Talata, a wani jawabi da ya fitar ta ofishin sakataren yaɗa labaransa, Mr. Chris Ita, ya sallami, Mr Francis Etta, daga kujerarsa.

KARANTA ANAN: Manyan Dalililai 5 da Suka Tabbatar da Mutuwar Shugaban Boko Haram, Abubakar Sheƙau

A jawabin da bai wuce sakin layi biyu ba, Ita yace:

"Mai girma gwamna, Farfesa Ben Ayade, ya amince da cire Hon. Francis Etta, kwamishinan ayyuka na musamman, daga muƙaminsa nan take."

"Gwamna ya gode masa bisa aikin da yayi wa jihar, kuma yana masa fatan alkairi a gaba."

Duk da cewa jawabin bai faɗi dalilin sallamar kwamishinan ba, amma ana ganin yana da dangantaka da ƙin bin gwamnan zuwa jam'iyyar APC.

A wani labarin kuma Babu Tantama APC Ce Zata Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a 2023, Inji Wani Jigo

Wani jigon jam'iyyar APC a jihar Delta kuma ɗan majalisar wakilai na tarayya yayi hasashen zaɓen shugaban ƙasa dake tafe.

Yace babu tantama APC mai Mulki ce zata sake ɗarewa kujerar shugabancin ƙasar nan, kuma PDP ta fara nuna damuwa da hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262