Sanatan APC bai yarda a sallamawa 'Yan Kudu mulki a bagas idan Shugaba Buhari zai sauka ba

Sanatan APC bai yarda a sallamawa 'Yan Kudu mulki a bagas idan Shugaba Buhari zai sauka ba

- Adamu Muhammad Bulkachuwa ba ya goyon-bayan yin tsarin karba-karba

- ‘Dan Majalisa yana ganin yin hakan ba zai haifar da ‘Dan takarar kwarai ba

- Sanatan na Bauchi ya na so jam’iyyu su bar kofar neman takara a bude a 2023

Sanata mai wakiltar yankin Bauchi ta Arewa a majalisar dattawa, Adamu Mohammed Bulkachuwa, ya yi magana game da yadda 2023 zai kasance.

Adamu Mohammed Bulkachuwa ya nuna cewa sam ba ya goyon-bayan tsarin karba-karba, ta yadda za a rika zagayawa da mulki tsakanin Kudu da Arewa.

Da yake magana a ranar Talata, 2 ga watan Yuni, 2021, Sanata Adamu Mohammed Bulkachuwa ya ce duk ‘dan siyasar da yake ganin zai kai labari, ya fito takara.

KU KARANTA: Buhari ya yi kunnen uwar-shegu da shawarwarin da nake ba shi – Bakare

“Ni tun farko ban yarda da tsarin karba-ka bani ba. A bar kofar neman takarar shugaban kasa a bude, duk wanda yake sha’awa, yake ganin ya dace, ya nema.”

“Duka jam’iyyun siyasa su fito da ‘dan takarar da ya fi nagarta, sai a bar ‘yan Najeriya su zabi wanda ya fi cancanta a cikinsu.” Inji Sanatan a shirin Politics Today.

‘Dan majalisar yake cewa: “Duk wanda yake tunanin ya cancanta, kuma zai iya samun kuri’a, ya shiga takara. Amma tsarin yi-ka-bani, ba abin kwarai ba ne a siyasa”

“Wadanda suka fi kuri’a, suka aminta da wani ‘dan takara, tabbas za su ci zabe. Sai dai idan kuma ba a son yin hakan, wanda hakan ya sabawa tsarin damukaradiyya.”

KU KARANTA: Boris Johnson ya angonce da Carrie Symonds a boye a Ingila

Sanatan APC bai yarda a sallamawa 'Yan Kudu mulki a bagas idan Shugaba Buhari zai sauka ba
Majalisar Dattawa Hoto:premiumtimesng.com
Asali: UGC

“Daga nan sai mutum ya nemi hanyar da yake ganin za ta fi bullewa, amma ni ban yarda cewa tsarin karba-karba shi ne zai kawo shugaban da ya fi dacewa ba.”

‘Dan majalisar mai shekara 81 ya yi wannan bayanin ne a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabiji na Channels TV, aka nemi jin ra’ayinsa kan zabe mai zuwa.

Kamar yadda jaridar The Boss Newspapers ta fitar da rahoto, da wannan ra’ayi na Bulkachuwa, mutumin Arewa zai iya kuma karbar mulkin Najeriya bayan 2023.

A baya kun ji cewa tun yanzu wasu manyan ‘yan siyasa da masu fashin baki sun fara lissafi game da babban zaben da za ayi a 2023, inda APC za ta gwabza da PDP.

Daga cikin jiga-jigan ‘yan siyasan Arewa da ake ganin cewa da su za a fafata a zabe mai zuwa akwai Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso da kuma Aminu Tambuwal.

Asali: Legit.ng

Online view pixel