Yanzu Yanzu: Fada ya kaure a tsakanin masu zanga-zangar goyon bayan Buhari a Abuja

Yanzu Yanzu: Fada ya kaure a tsakanin masu zanga-zangar goyon bayan Buhari a Abuja

  • Rikici ya kaure a tsakanin masu zanga-zangar goyon bayan Shugaba Buhari a Abuja
  • An tattaro cewa lamarin ya fara ne a kan rabon kudaden da aka tanada domin shirya zanga-zangar
  • Zanga-zangar dai na gudana ne a safiyar yau Asabar, 12 ga watan Yuni wanda yayi daidai da ranar damokradiyyar kasar

Wani rikici ya barke a safiyar ranar Asabar, 12 ga watan Yuni, a tsakanin mambobin kungiyar zanga-zangar goyon bayan Buhari wato #IStandWithBuhari a Unity Fountain, Abuja.

An ga shugabannin kungiyar suna musayar zafafan kalamai kan rabon kudaden da aka tanada domin gudanar da zanga-zangar adawar, jaridar Punch ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: A shirye nake da na mutu domin Najeriya: muhimman batutuwa 9 da Buhari ya gabatar a jawabin ranar Demokradiyya

Yanzu Yanzu: Fada ya kaure a tsakanin masu zanga-zangar goyon bayan Buhari a Abuja
Wasu daa cikin masu zangga-zanga dauke da rubutu daban-daban Hoto: Punch
Asali: UGC

Dangane da zanga-zangar ranar 12 ga watan Yuni, daruruwan magoya bayan Buhari sun isa Unity Fountain don nuna goyon bayansu ga Shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Yan sanda sun damke dan jaridar Legit.ng a Abuja

A gefe guda, jami'an yan sandan Najeriya sun damke mai daukan hoton Legit TV, Samuel Olubiyo, yayinda yake dauka rahoton zanga-zangan June12 dake gudana a birnin birnin tarayya Abuja.

Mun samu labarin cewa an dauke matashin ne yayinda yake daukan hotunan abubuwan dake gudana a filin zanga-zangan kuma aka kwace kamararsa.

A lokacin kawo muku wannan rahoton, duk wani yunkurin tuntunbarsa da sanin halin da yake ciki ya ci tura.

Wani mai idon shaida ya bayyana mana cewa an damke Samuel ne kuma an kaishe ofishin yan sandan Apo duk da cewa ya nuna musu shi dan jarida ne.

A wani labarin kuma, Shugaba Muhammadu ya bayyana yadda 'Yan Najeriya ke yaba masa a wata hira ta musamman da ya yi da Gidan talabijin na Kasa NTA a ranar Juma’a.

Shugaban ya ce gwamnatinsa na kokarin ganin kasar ta ci gaba da kasancewa kasa dunkulalliya tare da samar da abubuwan yau da kullun na rayuwa.

Shugaban ya kara da cewa zai tsaya tsayin daka kan rantsuwar da ya yi na yi wa ‘yan Najeriya aiki na gaskiya da kwazo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel