Duk wani Gwamna da ya bar PDP, ya shiga APC zai sha mamaki – Gwamnan Benuwai

Duk wani Gwamna da ya bar PDP, ya shiga APC zai sha mamaki – Gwamnan Benuwai

- Samuel Ortom ya fadi abin da ya sa wasu Gwamnonin PDP ke sauya-sheka

- Gwamnan Benuwai ya ce abokan aikinsa na komawa APC ne saboda EFCC

- Ortom ya na ganin a karshe hukuma za ta bi ta kamo wadanda suka yi sata

Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya yi hira da jaridar Vanguard, inda ya tabo batun siyasar da ake bugawa a APC da PDP da halin da kasa ta shiga.

Manema labarai sun yi wa Samuel Ortom tambaya game da gwamnonin da suke barin jam’iyyarsa ta PDP, suna sauya-sheka zuwa APC mai mulkin kasa.

Ya ce: “Na san harkar nan tun 1982, kusan shekaru 40 kenan. Ana yawan ganin irin haka. Wasunsu suna tsoron hukumar EFCC ne, shiyasa suke sauya-sheka.”

KU KARANTA:An kawo shawarar a hada tikiti tsakanin Atiku da Soludo

"Ku tuna cewa wani tsohon shugaban APC ya ce da zarar ka shigo jam’iyyarsu, an yafe maka zunubanka. Tsoron ayi ram da su ne ya sa su ke shiga APC.”

Vanguard ta rahoto gwamna Ortom ya na cewa akwai ranar kin dillanci, hukuma ba za ta ki cafke barayi ba. “Ba mu damu ba, za ku ga abin da zai faru a 2023.”

Gwamnan na Benuwai ya ce shi ba waliyyi ba ne, amma ya hango za a kama wadannan mutane nan gaba.

Duk da matsalar sauyin-shekar, Ortom ya na ganin ragowar gwamnonin PDP ne kurum suke kaddamar da ayyuka a kasar nan, domin sune su ka san kan aiki.

Duk wani Gwamna da ya bar PDP, ya shiga APC zai sha mamaki – Gwamnan Benuwai
Gwamnan Benuwai
Asali: UGC

KU KARANTA: Jami’an tsaro sun bindige Jagoran ‘Dan ta’addan IPOB

Kamar yadda mu ka samu labari, Ortom ya yi wannan jawabi ne bayan ya dawo daga jihar Oyo, inda ya kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin Seyi Makinde ta yi.

Gwamna Samuel Ortom ya bar APC ne a 2018, ya koma jam'iyyar PDP har kuma ya yi nasarar zarcewa a kan mulki. Kafin nan sai da ya rike Minista a gwamnatin PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel