2023: Atiku ya mayar da martani game da kudirinsa na shugabancin kasa, ya magantu kan fastocinsa da Soludo

2023: Atiku ya mayar da martani game da kudirinsa na shugabancin kasa, ya magantu kan fastocinsa da Soludo

- Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi watsi da fastocin yakin neman zabe da suka hada shi da Soludo a matsayin ‘yan takarar shugaban kasa da mataimakinsa

- Fastocin sun haifar da cece-kuce tsakanin mambobin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da APGA

- Abubakar ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 7 ga watan Yuni, a Abuja, ta hanyar wata sanarwa da mai taimaka masa ta fuskar yada labarai, Paul Ibe ya fitar

Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, ya yi watsi da fastocin yakin neman zaben shugaban kasa da suka hada shi da wani tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Charles Soludo a matsayin abokin takarar sa.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa fastocin, wadanda suka bayyana a Abuja a ranar Litinin, suna dauke da hotunan Atiku da Soludo a gefe suna sanar da tikitin Atiku / Soludo na zaben shugaban kasa na 2023.

KU KARANTA KUMA: Jami'an DSS suna neman Fasto Mbaka, bayan ya cigaba da caccakar Gwamnatin Buhari a mimbari

2023: Atiku ya mayar da martani game da kudirinsa na shugabancin kasa, ya magantu kan fastocinsa da Soludo
2023: Atiku ya mayar da martani game da kudirinsa na shugabancin kasa, ya magantu kan fastocinsa da Soludo Hoto: Atiku Abubakar.
Asali: Depositphotos

Legit.ng ta tattaro cewa Atiku a cikin wata sanarwa da ofishin yada labaran sa ya fitar da kuma sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya ce bai san komai ba game da fastocin ko kuma wadanda watakila suka yada shi.

Har yanzu ni dan jam’iyya PDP ne

Jaridar Premium Times ma ta ruwaito cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa har yanzu shi mamba ne na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Soludo kuma a yanzu haka yana tarakar kuerar ggwamna a zaben 6 ga watan Nuwamba a jihar Anambra, karkashin inuwar jam’iyyar All Progressive Grand Alliance (APGA).

KU KARANTA KUMA: Sarkin Musulmi: Wasu Tsirarun 'Sheɗanun' Manyan Mutane Na Ƙoƙarin Tarwatsa Nigeria

Ya ce:

“A bisa ƙa’ida, da mun yi watsi da rahotannin, amma don muradin waɗanda za su iya ɓata da maƙarƙashiyar. A bayyane yake cewa wannan aikin makirci ne. Don kaucewa shakka, Atiku Abubakar na PDP ne yayin da Charles Soludo na APGA. Wauta ce ga wani yayi yunkuri don jawo tsohon mataimakin shugaban kasar cikin zaben Anambra wanda mutanen jihar ne za su samar da sakamakon shi."

Atiku ya sake nanata cewa wasu fastocin kamfe din 2023 da ake yadawa wadanda ke alakanta shi da Soludo aikin makirai ne kuma ya kamata a yi watsi da shi.

Magoya bayan Atiku sun yi sammako, sun fara yi masu yakin neman Shugaban kasa tun yanzu

A wani labarin, mun ji cewa Kungiyar magoya bayan Atiku Abubakar da Charles Soludo sun kaddamar da yakin neman zaben 2023.

Jaridar Daily Trust ta ce magoya bayan Atiku Abubakar da Farfesa Charles Soludo sun soma yi masu fafatukar zaba shugaban kasa a 2023.

Wajen kaddamar da wannan shiri a yau, 7 ga watan Yuni, 2021, a garin Abuja, shugaban tafiyar, Kwamred Andy Ekwe, ya bayyana manufarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng