Masu garkuwa da mutane sun dawo, sun rage kudin fansar Dalibai 156 da aka sace a Islamiyya

Masu garkuwa da mutane sun dawo, sun rage kudin fansar Dalibai 156 da aka sace a Islamiyya

- ‘Yan bindigan da suka yi garkuwa da yara 156 sun rage kudin fansar da suka lafta

- Migayun sun bukaci yanzu a aiko Naira Miliyan 150 tun da Miliyan 200 ta gagara

- Wani karamin yaro daga cikin ‘yan makarantar da aka sace ya mutu a hannunsu

‘Yan bindigan da suka yi awon-gaba da dalibai 156 daga makarantar Islamiyyar Salihu Tanko Islamiyya sun rage kudin da suke bukata a matsayin fansa.

Miyagun da suka dura Salihu Tanko Islamiyya School a Tegina, karamar hukumar Rafi, a jihar Neja, sun ce a biya N150m domin su fito da ‘yan makarantan.

This Day ta ce da farko ‘yan bindigan sun lafta N110m a kan wadannan ‘yan makaranta, daga baya sai suka kara kudin, suka ce dole sai an aiko masu da N200m.

KU KARANTA: Tsohon da aka yi tunani ya mutu shekaru aru-aru ya dawo gida

Abin da ‘yanuwa da iyayen wadannan ‘yan makaranta suka iya tattara wa suka kai wa ‘yan bindigan shi ne N11.6m, miyagun ba su karbi wannan kudi ba.

Shugaban wannan makarantar Islamiyya, Alhaji Abubakar Alhassan, ya tabbatar da wannan labari, ya ce iyaye da hukumar makaranta suna ta kokarin ceto yaran.

“Muna kira ga gwamnatin tarayya da na jihohi su kawowa iyayen nan agaji Babu wanda zai iya biyan kudin da aka bukata sai gwamnati.” Inji Malam Alhassan.

Alhassan ya ce ‘yan bindigan sun ba shi damar magana da daya daga cikin yaran da aka dauke. Malamin ya ce wannan daliba ta fada masa duk suna nan kalau.

Masu garkuwa da mutane sun dawo sun rage kudin fansar Dalibai 156 da aka sace a Islamiyya
Gwamna Abubakar Sani Bello Hoto: @GovNiger
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun bada wa'adin biyan kudin fansa a Tegina

A cewar wannan Baiwar Allah wanda ita ta manyanta cikin wadanda aka yi garkuwa da su, babu abin da ake ba su a matsayin abincinsu dare da rana sai kuli-kuli.

Kusan makonni biyu da suka wuce ne aka yi garkuwa da wadannan yara, daga ciki har da wani mai shekara uku wanda jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ya mutu.

Kamar yadda daya daga cikin iyayen yaran, Tanko Zegi, ya shaidawa manema labarai, zazzabi da tashin hankalin jin karar bindiga ne ya yi sanadiyyar mutuwar yaron.

Kwanakin baya kun samu labarin cewa 'yan bindigan da suka sace yaran n makarantar Islamiyya a Tegina sun sako wasu daga cikinsu saboda sun yi kankanta.

Sakatariyar watsa labarai ta gwamnan jihar Neja, Noel-Berje, ta tabbatar da wannan, ta ce an saki yara 11 daga cikin daliban da aka sace saboda tsoron su zama alakalai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng