Bakare: Abubuwa sun birkice, zama da Buhari, da shi da babu duk daya, na daina zuwa Aso Villa

Bakare: Abubuwa sun birkice, zama da Buhari, da shi da babu duk daya, na daina zuwa Aso Villa

- Fasto Tunde Bakare ya bayyana alakarsa da Shugaba Muhammadu Buhari

- Limamin cocin ya ce zaman da yake yi da Shugaban kasar ba ya yin tasiri

- Wannan ya sa Fasto Tunde Bakare ya ce ya daina zuwa ya zauna da Buhari

Shugaban cocin Citadel Global Community wanda a baya aka sani da Latter Rain Assembly, Tunde Bakare, ya ce sam shugaban kasa ba ya sauraronsa.

Jaridar The Cable ta ce Fasto Tunde Bakare ya koka a kan cewa shugaba Muhammadu Buhari ba ya daukar maganganun da ya fada masa domin kawo gyara.

Tunde Bakare wanda ya yi takarar kujerar mataimakin shugaban kasa tare da Muhammadu Buhari a CPC ya ce ya gaji da zama da shugaban Najeriyar.

KU KARANTA: Samun mulki ya canza Buhari - Tunde Bakare

Da yake magana da BBC Yoruba, Fasto Bakare ya ce shugabannin Najeriya ba su da gaskiya, ya zarge su da jefa al’ummar kasar nan a cikin halin da ake ciki.

Bakare yake cewa mutane sun zabi Muhammadu Buhari ne da tunanin cewa a matsayinsa na tsohon soja, ya san yadda zai shawo kan matsalolin kasar nan.

“Abubuwa sun birkice ta bai-bai. Sun ce manya suke kashe kasa, amma da matasa aka soma. Wadanda suka yi juyin-mulkin soja– ‘yan shekara 20-30 ne.”

“Sune suka jefa mu a halin da mu ke ciki a yau. Su suka jawo mana wannan, sannan kuma suka ki hakura su tafi, su bar mulki bayan sun tsufa.” Inji Bakare.

KU KARANTA: Maganar sauya-shekar Gwamna Matawalle zuwa APC ta na ta kara karfi

Bakare: Abubuwa sun birkice, zama da Buhari, da shi da babu duk daya, na daina zuwa Aso Villa
Fasto Tunde Bakare Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Bakare yake cewa a gidansa aka fara tsara tafiyar Save Nigeria Group domin a ceto mutanen Najeriya, ya ce a lokacin bai san shugaba Jonathan ko Yar’Adua ba.

A wannan tafiya ne Faston ya ci karo da Muhammadu Buhari, ya jawo shi kusa, har suka hadu a Kaduna. A karshe suka yi takarar shugaban kasa tare a zaben 2011.

“Buhari mutum ne wanda na saba zuwa in hadu da shi, zai saurare ka, amma da zarar ka tafi, shikenan babu abin da za a yi. Sai na zabi in tsaya a gefe.” Inji shi.

Kwanaki kun ji cewa Tunde Bakare, ya bayyana aniyarsa na zama shugaban kasar Najeriya. Bakare ya ce idan da dama, zai so ya gaji shugaba Muhammadu Buhari.

Bakare ya ce ba batun 'a mutu ko ayi rai ba ne', amma ya na yi wa kansa kallon irin abin da ya faru da Joe Biden wanda ya zama shugaban Amurka bayan ya tsufa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel