APC ta gargadi 'yan Najeriya kan illolin amfani da VPN wajen hawa Twitter

APC ta gargadi 'yan Najeriya kan illolin amfani da VPN wajen hawa Twitter

- Jam'iyyar APC a Najeriya ta shawarci 'yan Najeriya kan su daina amfani da VPN wajen hawa Twitter

- Jam'iyyar ta bayyana illolin da ke tattare da amfani da VPN wajen hawa shafukan yanar gizo baki daya

- Jam'iyyar ta kuma bayyana tsoron cewa, ana iya satar bayanai da kudaden mutum ta amfani da VPN din

Jam’iyyar APC ta fadakar da ‘yan Najeriya game da hadurran da ke tattare da samun bayanai, musamman a kafofin sada zumunta ta amfani da Virtual Private Network (VPN).

Sanarwar ta ce yana da matukar sauki ga munanan ayyukan masu satar bayanai wadanda za su iya satar bayanai da kudade a asusun banki su sauka kan 'yan Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Sakataren kwamitin kula na rikon kwarya na jam'iyyar APC, Sanata John James Akpanudoedehe ne ya bayyana haka a ranar Talata.

KU KARANTA: Bayan korar dukkan kwamishinoninsa, gwamna Matawalle ya dawo da 3 daga cikinsu

APC ta gargadi 'yan Najeriya kan illar amfani da VPN wajen hawa Twitter
APC ta gargadi 'yan Najeriya kan illar amfani da VPN wajen hawa Twitter Hoto: bbc.com
Asali: UGC

“An shawarci wadanda ke amfani da VPN da su daina saboda kasadar da yake kunshe dashi, wadanda suka hada da satar bayanai, shiga haramtattun takardu na wani kamfani da kuma leken asirin tattalin arziki.

“Jam’iyyar APC ta jaddada cewa masu amfani da VPN suna ba da damar kutse ga na'urorinsu saboda hanyar sadarwar na baiwa wasu kamfanoni damar samun bayanan sirri da kuma canza wurin masu amfani da su zuwa wata kasa wacce ke lalata ingancin bayanan.

“Ana iya gano kasancewarka a wata kasa wacce ba taka ba, tare da duk hadarin da ke tattare da hakan.

“Mutane da yawa da kungiyoyi masu amfani da VPN sun rasa jarinsu bayan sun lalata tsaron na'urorinsu.

Wannan yasa jam'iyyar ta ke shawartar 'yan Najeriya da su guji amfani da VPN wajen hawa shafin Twitter.

A makon da ya gabata ne gwamnatin Najeriya ta dakatar da ayyukan Twitter a kasar bayan da ta zargi shafin da karfafa rikice-rikice a kasar.

Sai dai, yawancin 'yan Najeriya suna amfani da Twitter ta hanyar VPN da sauran hanyoyin daban, BBC ta ruwaito.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Jami'ar Kaduna ta KASU ta dakatar da karatun digiri na farko

A wani labarin, Majalisar Wakilai ta zartar da bincike kan shawarar da Gwamnatin Tarayya ta yi na hana ayyukan Twitter a Najeriya.

Ta ce za ta kuma yi la’akari da tsarin shari’ar da Gwamnatin Tarayya ta bi wajen yanke hukunci a kai, The Nation ta ruwaito.

Najeriya a ranar Juma’a ta dakatar da ayyukan Twitter, kwanaki biyu bayan da kamfanin na sada zumunta ya cire wani rubutu na Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya yi barazanar hukunta masu rigimar ballewa daga Najeriya, Reuters ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel