Ba Dan Najeriya Mai Hankali Da Zai So Mulkin Dan Kudu Maso Gabas, Sumaila

Ba Dan Najeriya Mai Hankali Da Zai So Mulkin Dan Kudu Maso Gabas, Sumaila

- Wani tsohon hadimin shugaba Buhari ya bayyana dalilin da zai sa dan Najeriya ba zai zabi dan kudu maso gabas ba

- A cewarsa, 'yan yankin kudu maso gabas sun yi shuru kan barnar da IPOB ke aikatawa, don haka ba abin yarda bane su

- Hakazalika ya shawarci fitattun mutane daga yankin su fito su bayyana matsayinsu kan abubuwan da ke faruwa

Wani tsohon hadimin Shugaba Buhari, kan lamuran Majalisa, Abdurrahman Sumaila, ya ce ‘yan Najeriya masu tunani ba za su jefa rayukansu cikin hadari ba don mara wa takarar duk wani dan siyasar Kudu maso Gabas da ke neman shugabancin kasar nan a 2023 ba.

Sumaila ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kano ranar Alhamis, jaridar Punch ta ruwaito.

“Tare da wadannan munanan dabi’un da mutanen Kudu-maso-Gabas suka aikata, ta yaya 'yan Najeriya za su ba su amanar su shugabance mu?

KU KARANTA: Rahoto: An Gargadi Ahmed Gulak Kada Ya Tafi Imo, Amma Ya Yi Biris

Ba Dan Najeriya Mai Hankali Da Zai So Mulkin Dan Kudu Maso Gabas Ba, Sumaila
Ba Dan Najeriya Mai Hankali Da Zai So Mulkin Dan Kudu Maso Gabas Ba, Sumaila Hoto: muryararewa.ng
Asali: UGC

"Ina da yakinin babu wani dan Najeriya mai cikakken tunani da zai jefa rayuwarsa cikin hadari don tallafa wa takarar duk wani dan siyasa na Kudu maso Gabas da zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben shekara ta 2023,” inji shi.

Da yake martani kan yawaitar hare-hare a yankunan kudu maso gabashin kasar, Sumaila ya zargi 'yan yankin da kokarin kawo firgici da hargitsa kasar ba gaira da dalili.

Ya kuma lura cewa dalilin kai wadannan hare-hare shi ne jefa kasar cikin rudani, yana mai nadamar cewa "masu yin wadannan hare-hare dole ne su fahimci cewa idan kasar ta rikide ta zama hargitsi, to babu wanda zai tsira har da masu aikata hakan."

Don haka, ya bukaci dattawa a yankin Kudu Maso Gabas da su fito fili su yi tir da hare-haren da ake zargin mambobin kungiyar IPOB na yi ko kuma a dauke su da hannu dumu-dumu cikin wannan mummunan aiki.

Sumaila ya kuma ce dole ne shugabannin kudu su tabbatar da matsayinsu, idan ba haka ba 'yan Najeriya za su dauke su a matsayin wani bangare na hare-haren da 'yan bindiga ke kaiwa a yankin.

“Ya kamata fitattun mutane a yankin Kudu maso Gabas suyi koyi da takwarorinsu na Arewa kamar su Zauren Tuntuba na Arewa da Zauren Dattawan Arewa, wadanda ke ci gaba da yin tir da ayyukan mayakan Boko Haram da yan bindiga a Arewa,” in ji shi.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Afkawa Bankuna Da Ofishin 'Yan Sanda, Sun Yi Barna Sun Tsere

A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda ta yi gargadin cewa mambobin haramtacciyar kungiyar IPOB na ganawa a wasu sassan jihar Edo don yada burinsu na ballewa a fadin jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Mataimakin Sufeto-Janar na ’yan sanda da ke kula da aikin dawo da zaman lafiya a yankin Kudu-maso-Kudu, Moses Jitoboh, ya bayyana haka ne a jiya Laraba a lokacin kaddamar da aikin a Garin Benin.

Ya ce a yanzu haka ‘yan kungiyar IPOB suna gudanar da taron sirri a Igbanke, Ubiaja, Iguelaba, Igueben, Okhiahe da Ologbo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel