Kano: Kotun Shari’ar Musulunci Ta Tilasta Matashi Share Babban Masallacin Juma’a
- Wata kotun shari’ar Musulunci a Kano ta ba da umarni ga wani matashi da ya je babban masallacin Juma'a a jihar domin share shi
- Kotun ta kuma umarce shi da halartar sallolin farilla guda biyar a cikin jam’i kullum, bayan ya amsa laifin haɗa baki da sata
- Rahotanni sun nuna cewa an kama Sheka tare da abokinsa bisa zargin satar fitilun titi a unguwar Sallare, amma abokin nasa ya tsere
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Abin mamaki bai karewa a Najeriya, ana zargin wani matashi da sace fitilun titin unguwarsu wanda gwamnati ta samar masu.
Bayan zarginsa ne, wata kotun shari’ar Musulunci a Kano ta umarci wani matashi, Ahmad Salisu Sheka, da share Masallacin Juma’a na Murtala Mohammed.

Source: Facebook
Rahoton da muka samu daga Daily Trust ya ce bayan haka, kotun ta umarci matasin da ya halartar sallolin farilla guda biyar a cikin jam’i kullum.

Kara karanta wannan
Abin mamaki: An tsinci gawar magidanci da wani irin rauni a al'aurarsa, matarsa ta gudu
Kotu ta raba auren Sunnah a Ramadan
Ko a kwanakin baya ma, mun ba ku labarin cewa wata Kotun Shari'ar Musulunci aKano ta yi nasarar raba wasu ma'aurata.
Kotun shari'ar Musulunci a jihar Kano ta raba auren Shamsiyya da Ghali bayan duk wani yunƙurin na yin sulhu ya ci tura.
A zaman yanke hukunci a ranar Alhamis, 14 ga watan Maris, mai shari'a Malam Umar Lawal Abubakar, ya datse igiyoyin auren sabida mijin ya bar gida.
Tun farko magidancin ya shaidawa Alkali cewa ya gudu ya bar gida ne saboda halin matsin da ake ciki kuma ya rasa motar da yake tuƙawa.

Source: Original
Matashin ya tabbatar da aikata laifin
Kotun Shari’ar Musulunci ta sama da ke Hausawa, Filin Hockey, Kano, ƙarƙashin jagorancin Dr Bello Musa Khalid, ta yanke wa Sheka hukunci ne bayan ya amsa laifukan haɗa baki da sata.
Bayan ya amsa laifin, kotun ta tabbatar da laifinsa ta hanyar furucin da ya yi, kafin ta yanke masa hukuncin share masallacin da halartar sallolin farilla guda biyar a cikin jam’i.

Kara karanta wannan
Asiri ya tonu: An kama wasu matasa 2 da ba a yi tsammani ba ɗauke da bindiga a Kano
Kotun ta kuma umarce shi da biyan diyya kafin ta miƙa shi ga wani jami’in gidan gyaran hali, Habib H. Habib, domin aiwatar da hukuncin.
Rahotanni sun nuna cewa an kama Sheka tare da abokinsa bisa zargin satar fitilun titi a unguwar Sallare da ke Kano.
Sai dai an ruwaito cewa abokin nasa ya tsere daga hannun mutanen da suka kama su wanda har yanzu ba a yi nasarar cafke shi ba.
Kotun Musulunci ta raba masoya a Kaduna
A baya, mun kawo muku rahoton cewa Kotun Shari’ar Musulunci da ke Rigasa ta hana wani matashi suna Salisu Salele kusantar tsohuwar budurwarsa, Bilkisu Lawal.
Mai shari’a Salisu Abubakar-Tureta ya ce daga yau, Salisu ba zai kira ko gana da Bilkisu ba, kuma haramun ne ya bi unguwarsu.
Salisu ya ce yana son Bilkisu amma ba zai iya aure yanzu ba har sai bayan shekaru biyu, domin yana karatu kuma bai da kudin sadaki.
Asali: Legit.ng