Bayan Ganawa da Tinubu, An Ji Lokacin da Gwamnan Bauchi Zai Bar PDP zuwa APC

Bayan Ganawa da Tinubu, An Ji Lokacin da Gwamnan Bauchi Zai Bar PDP zuwa APC

  • Gwamna Bala Mohammed ya kammala shirin barin PDP zuwa APC a wannan makon bayan tattaunawa da Shugaba Bola Tinubu kan makomarsa
  • An rahoto cewa Shugaba Tinubu ya gargaɗi Bala Mohammed cewa ba zai ba shi ikon zaɓar wanda zai gaje shi ba koda ya koma jam'iyyar APC
  • An kuma umarci Gwamna Bala ya ba ɗan shugaba ƙasa Seyi Tinubu haƙuri kafin a amince da buƙatarsa ta shiga cikin jam'iyyar mai mulki a ƙasa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Bauchi - Rahoto ya ya nuna cewa jam'iyyar adawa ta PDP na iya fuskantar rugujewa baki ɗaya, sakamakon kammala shirin Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi na komawa jam'iyyar APC a wannan makon.

Bala Mohammed, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin PDP, ya gana da Shugaba Bola Tinubu da shugabannin APC inda ya bayyana aniyarsa ta shiga jam'iyya mai mulki a ƙasa.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun farmaki sakataren kungiyar Izala a inda yake tafsirin Alkur'ani

Ana zargin gwamnan Bauchi zai koma jam'iyyar APC a makon da za a shiga.
Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed (hagu) da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu (dama). Hoto: @SenBalaMohammed, @officialABAT
Source: Facebook

Gwamnan Bauchi na shirin barin PDP

Duk da cewa har yanzu ana tattaunawa kan sharuɗɗan sauya shekarar, amma majiyoyi sun bayyana wa Arise News cewa an yi masa alkawarin tikitin takarar Sanata.

Sai dai, an ba shi wasu tsauraran sharuɗɗan da suka bambanta da na sauran gwamnonin da suka sauya sheka a baya, lamarin da ke nuna cewa lissafin siyasar jihar Bauchi na iya sauyawa.

Majiyoyi sun bayyana cewa shirin sauya shekarar Gwamna Bala na iya samun alaƙa da matsin lambar da kwamishinan kuɗin Bauchi, Yakubu Adamu, ke fuskanta, wanda ake zargi da tallafa wa ta'addanci da kuma karkatar da kuɗi har NN4.6bn.

Sharudan da aka kafawa Bala na shiga APC

A yayin ganawar, Shugaba Tinubu ya nuna cewa ba za a ba Bala Mohammed ikon juya akalar jam'iyyar APC a Bauchi baki ɗaya ba, sannan ba za a ba shi damar zaɓar wanda zai gaje shi ba.

Kara karanta wannan

Hadimin Osinbajo ya raba wa ADC gardama, ya fadi mutum 2 da suka dace da yin takara a 2027

Bayan haka, an umarci gwamnan da ya ba ɗan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu, haƙuri kan kalaman da ɗan gwamnan, Shamsudeen Bala, ya yi a watan Maris 2025 inda ya soki rabon kayan abinci da Seyi ya yi a Bauchi.

Rahotanni sun ce tuni gwamnan ya ba da wannan haƙuri don ganin cewa hakan bai zama kalubale gare shi na komawa jam'iyyar APC ba.

Hakazalika an ce gwamnan na neman shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya tattauna da shugaban ƙasa don ba shi kaso 40 cikin 100 na ikon jam'iyyar a jihar, maimakon hana shi komai.

Gwamnan Bauchi na shirin barin PDP zuwa APC.
Tutar jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya. Hoto: @OfficialAPCNg
Source: UGC

Bangaren Gwamna Makinde sun nuna mamaki

Bangaren gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya nuna tsananin mamaki da takaicin yadda gwamnan da ke jagorantar gwamnonin PDP zai mika wuya ga jam'iyyar APC.

Bangaren Makinde na ikirarin cewa Gwamna Bala ne ake zargin ya rura wutar rashin jituwa a cikin PDP tsawon shekaru ta hanyar taurin kansa.

A halin yanzu, Gwamna Bala Mohammed ya kira taron masu ruwa da tsaki a jihar Bauchi a wannan makon domin sanar da matsayarsa, yayin da yake jiran ganin ko Shugaba Tinubu zai sassauta masa kan sharadin zaɓar wanda zai gaje shi.

Kara karanta wannan

Iran ta ji wuta, ta shirya mika wuya ga Amurka? Trump ya yi magana

Gwamna Bala ya musanta barin PDP

Tun da fari, mun ruwaito cewa, gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya yi magana kan yiwuwar barin jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya.

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa ba shi da wani shiri na barin jam’iyyar PDP wadda ya lashe kujerar gwamna sau biyu a karkashinta.

Gwamna Bala, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin PDP, ya ce mutanen jihar Bauchi ne suka zaɓe shi a matsayin gwamna har sau biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com