Bayan Maganganu Sun Yi Yawa, Tinubu Ya Yi Bayani kan Batun Murkushe Adawa a Najeriya
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan batun jefarsa da ake yi da zargin yunkurin murkushe adawa a Najeriya
- Mai girma Bola Tinubu ya bayyana cewa masu sukarsa suna da 'yanci da damar fadin ra'ayoyinsu da albarkacin bakinsu
- Shugaban kasar ya nuna cewa ba zai ga laifin duk wani dan siyasa da ya fice daga jam'iyyar da ke shirin rugujewa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan zarge-zargen cewa yana yunkurin kashe adawa a Najeriya.
Shugaba Tinubu ya musanta zarge-zargen da ake yi na cewa shi ne ke rura wutar sauya sheƙar mambobin jam’iyyun adawa zuwa jam’iyya mai mulki ta APC ba.

Source: Twitter
Shugaba Tinubu ya yi waɗannan kalaman ne a ranar Laraba, 25 ga watan Fabrairun 2026 a cikin bidiyo da shafin Nigerian Affairs Journal ya sanya a X.

Kara karanta wannan
Babu wasa: Sabon shugaban 'yan sanda ya sanar da 'yan Najeriya shirinsa bayan fara aiki
Mai girma shugaban kasar ya yi magana ne yayin taron buɗan bakin Ramadan na addinai daban-daban da ya yi da mambobin majalisar dattawa a fadar Aso Rock Villa.
Me Tinubu ya ce kan murkushe adawa?
Shugaba Tinubu ya maida martani kan iƙirarin da ake yi na cewa gwamnatinsa tana ƙoƙarin raunata jam’iyyun adawa.
Mai girma Bola Tinubu ya jaddada cewa bai tursasa wa kowa barin jam'iyyarsa ta siyasa ba.
Yayin da yake mayar da martani ga masu suka Tinubu ya ce suna da damar faɗar ra’ayoyinsu, amma ya yi watsi da zargin cewa ya aikata wani kuskure.
Tinubu bai ganin laifin masu sauya sheka
Ya ƙara da cewa ba zai ga laifin ’yan siyasar da suka zaɓi sauya sheƙa ba, inda ya kwatanta matakin nasu da barin “jirgin da ke nutsewa,” yayin da ya nuna ayyukan ta’addanci da 'yan bindiga a matsayin manyan ƙalubalen da ke rura wutar takaddamar siyasa.
“Dole ne masu suka su yi magana. Lokacin da suka zarge ni da kashe adawa, ai ba ni da bindiga. Da ina so, da na ba wa kaina lasisin mallakar bindiga tunda ina da ikon yin hakan."
“Amma ba zan iya zargin kowa ba idan ya tsallake daga jirgin da ke nutsewa. Abubuwan da muka fuskanta a wannan mawuyacin lokaci na kasarmu, kamar ta’addanci da 'yan bindiga, suna yi mana illa sosai."
- Shugaba Bola Tinubu

Source: Facebook
Tinubu ya ba 'yan siyasa shawara
Shugaban kasar ya bukaci shugabannin siyasa da su sanya haɗin kai a gaba daidai da burin magabatan da suka kafa Najeriya, inda ya jaddada cewa tsarin dimokuraɗiyya na kundin tsarin mulki an yi shi ne domin samar da haɗin kai maimakon rikici.
“Ya kamata mu haɗa ƙarfi da ƙarfe, mu kasance tsintsiya madaurinki ɗaya kamar yadda magabatanmu suka yi niyya domin samar da dimokuraɗiyya ta tsarin mulki da za ta haɗa kanmu. Ba su ce mu yi faɗa ba. Abu ne mai kyau da muke aiki cikin jituwa.”
- Shugaba Bola Tinubu
Tinubu ya mika bukatarsa ga majalisa
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika bukatarsa ga majalisar dattawan Najeriya.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci majalisar kasa da ta fara shirin gyara kundin tsarin mulki domin samar da ’yan sandan jihohi.
Mai girma Bola Tinubu ya ce gyaran kundin tsarin mulki ya zama dole domin a kare dazuzzuka daga hannun masu laifi.
Asali: Legit.ng
