Sabon Rikici: Gwamna Alia da Sakataren Gwamnatin Tinubu Sun Raba APC Gida 2
- Rahotanni sun nuna cewa taron zaɓen sababbin shugabannin unguwanni na jam'iyyar APC ya bar baya da kura a jihar Benue
- An bayyana cewa gwamnan jihar, Hyacinth Alia ya fitar jerin shugabannin da ya ce su aka zaba a dukkan kananan hukumomi
- Sai dai a daya bangaren kuma, sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ya fitar da jerin shugabanni na dabam
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Benue - Taraon zaɓen shugabannin unguwanni na jam’iyyar APC da ɓangarorin da ke biyayya ga gwamna Hyacinth Alia da sakataren gwamnatin tarayya (SGF), George Akume, suka shirya ya kammala a Benue.
Bayan kammala taron, kowanne ɓangare ya sanar da nasa shugabannin unguwanni a dukkan ƙananan hukumomi 23 na jihar Benue.

Source: Facebook
Shugabannin APC bangaren Akume
Daily Trust ta wallafa cewa taron ya haifar da sakamako mabambanta, inda tsagin da Austin Agada ke jagoranta kuma ke yi wa Akume biyayya ya sanar da tsarin da ya bi.
A karkashin tsarin, an bayyana cewa an sake tabbatar da tsofaffin shugabannin unguwanni domin su ci gaba da wa’adin shekaru huɗu.
Sakataren yaɗa labarai na ɓangaren, Daniel Ihomun, ya ce taron ya gudana cikin lumana kuma bisa umarnin uwar jam’iyya a matakin ƙasa.
Ihomun ya taya shugabannin da aka sake tabbatarwa murna, tare da ƙarfafa musu gwiwa su tabbatar da amincewar da mambobin jam’iyya suka nuna musu.
Shugabannin APC bangaren Alia
A ɗaya ɓangaren kuma, ɓangaren da ke goyon bayan Gwamna Alia ƙarƙashin jagorancin Benjamin Omale ya sanar da cewa an zaɓi sababbin shugabannin unguwanni ta hanyar yarjejeniya.
Mai magana da yawun kwamitin riƙo da ke biyayya ga gwamnan, James Ornguga, ya ce wa’adin shugabannin unguwanni, ƙananan hukumomi da na jiha ya ƙare, don haka dole ne a gudanar da sabon zaɓe.
Punch ta wallafa cewa Ornguga ya yi watsi da batun sake tabbatar da tsofaffin shugabanni, yana mai cewa babu wata ƙa’ida da ta ba da damar komawar su kai tsaye.

Kara karanta wannan
Kwana ya kare: Ana jimamin rasuwar Sanata Mpigi, Najeriya ta sake yin babban rashi

Source: Facebook
Ya jaddada cewa wa’adin shugabannin unguwanni ya ƙare a watan Yuli 2025, na ƙananan hukumomi a Satumba 2025, yayin da na jiha ya ƙare a ranar 8 ga Fabrairu, 2026, don haka sabon zaɓe ya zama dole.
A halin yanzu, ɓangarorin biyu sun nace cewa dukkan matakan da suka ɗauka sun yi daidai da ƙa’idojin jam’iyya, lamarin da ya bar jam’iyyar APC a Jihar Benue da shugabanni biyu.
An lakadawa 'yan APC duka a Ondo
A wani labarin, kun ji cewa wasu 'yan daba sun lakadawa 'yan jam'iyyar APC duka yayin da suke gudanar da zaben shugabannin unguwanni a jihar Ondo.
Rahotanni sun nuna cewa 'yan daba sun yi amfani da wukake da bindiga wajen kai farmaki, inda suka harbi kanin shugaban jam'iyyar tare da sara shi da adda.
Dattawan APC a jihar Ondo sun yi Allah wadai da harin da aka kai suna kira da cewa a dauki mataki domin ba a gina jam'iyyar kan ta'addanci ba.
Asali: Legit.ng
