Gwamna Mai-Ci ya ce Shugabannin da Ke Goyon Bayan Tsohon Gwamna Sun Shiga Uku

Gwamna Mai-Ci ya ce Shugabannin da Ke Goyon Bayan Tsohon Gwamna Sun Shiga Uku

  • Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara ya ce shugabannin kananan hukumomin jihar dake goyon bayan tsohon Gwamnan Jihar, Wike sun jefa kansu cikin matsala
  • Fubara bayyana haka cikin mamakin yadda wani shugaban karamar hukuma ya halarci taron kaddamar da asibitin sha-ka-tafi a jihar
  • Mai girma Gwamna ya yi wa shugaban karamar hukumar shaguɓen cewar yanzu sai a iya korarsa sakamakon halartar taron da ya yi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ribas - Gwamna Siminalayi Fubara ya caccaki shugabannin ƙananan hukumomin da ba su biyayya gare shi, inda ya ce suna daf da afkawa ramin da suka haƙa.

Kara karanta wannan

Shugabanci: An faɗi wanda ya cancanci zama sabon shugaban jam'iyyar PDP daga Arewa

Fubara ya bayyana hakan ne lokacin da yake ƙaddamar da asibitin sha-ka-tafi a Ndoni, a ƙaramar hukumar Gona/Egbema/Ndoni a jihar a Alhamis ɗin nan kamar yadda rahoton Daily Trust ya bayyana.

Gwamna Siminalayi da tsohon Gwamna Wike
Gwamna Fubara na zargin shugabannin kananan hukumomin da yi masa rashin ladabi Hoto: Sir Simialayi Fubara
Asali: Facebook

Gwamnan yana tsaka da ƙaddamar da asibitin ne sai ya hango shugaban ƙaramar hukumar Onelga, wanda hakan ya ba shi mamaki matuƙa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabannin ƙananan hukumomi da Gwamna Fubara

Gwamna Fubara ya ce yana sane da yadda shugabannin ƙananan hukumomin jihar suka daina halartar duk wani taro da aka shirya a matakin jiha.

Ya ce yana sane da cewa suna yin hakan ne saboda goyon bayansu ga tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike kamar yadda leadership news ta ruwaito.

A cewar Gwamnan:

"Na yi mamaki sosai da na ga shugaban ƙaramar hukumar Gona/Egbema/Ndoni a nan yau. Na yi mamaki saboda a wani lokaci yanzu, shugabannin ƙananan hukumomin na gujewa duk wani taro da muka shirya a matakin jiha.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya aike da muhimmin saƙo bayan kammala ƙaramar Sallah a Najeriya

Ina fatan idan ya bar nan yau ba za su kore shi ba."

Fubara ƙara da cewa:

" Na san ba ka goyon baya na. Ba za su kore ka ba? Ko idan ka bar nan za ka yi taron manema labarai ka ce ba kai ba ne. Inuwar ka ce.

Ana takun saƙa tsakanin Fubara da Wike

Duk da ƙoƙarin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi wajen sasanta rikicin dake tsakanin Nyesom Wike da Gwamnan Ribas mai ci a yanzu, Siminalayi Fubara, har yanzu tsuguno ba ta ƙare ba.

Wike yana zargin Fubara da ƙoƙarin ruguza tsarin siyasar da ya kafa a jihar Ribas na tsawon shekaru takwas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel