EFCC Za Ta Gurfanar Da Tsohon Gwamna Kan Wani Laifin Da Ya Aikata Lokacin Yana Ofis

EFCC Za Ta Gurfanar Da Tsohon Gwamna Kan Wani Laifin Da Ya Aikata Lokacin Yana Ofis

  • Hukumar EFCC za ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Anambra bisa zargin ya karkatar da naira biliyan hudu
  • Tun a shekarar 2022 ne hukumar ta fara kama Mr Obiano a filin jirgin sama yana shirin barin kasar, awanni bayan sauka daga mulki
  • EFCC ta sha alwashin sake duba duk wasu manyan laifuka da aka yi watsi da su musamman wadanda ya shafi tsaffin gwamnoni

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Awka, Anambra - Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) za ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, a ranar Laraba, 24 ga watan Janairu.

EFCC za ta gurfanar da Obiano a gaban mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa zargin almundahanar kudi har naira biliyan hudu.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya nuna gwamnan arewa 1, ya bayyana ayyukan Alherin da Yake Zuba Wa Talakawa

EFCC za ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Anambra
Badakalar naira biliyan 4: EFCC za ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Anambra. Hoto: @WillieMObiano, @officialEFCC
Asali: Twitter

Wakilin jaridar Punch ya tattaro a ranar Talata cewa za a gurfanar da tsohon gwamnan a gaban kuliya bisa laifuka tara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan mako guda da shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya sha alwashin sake duba duk wasu manyan laifuka da aka yi watsi da su, musamman wadanda suka shafi tsofaffin gwamnoni da ministoci.

Laifin da ake tuhumar Obiano ya aikata

Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa:

“Mun gano cewa Obiano ya kwaso naira 4,008,573,350 daga asusun jami’an tsaro zuwa asusu daban-daban."

Babban lauyan EFCC, Slyvanus Tahir, SAN, zai jagoranci wasu lauyoyi takwas a shari'arsu da tsohon gwamnan.

Ko da aka tuntubi mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da ya ce za a gurfanar da Obiano a ranar Laraba, shafin The Eagle ya wallafa.

Kara karanta wannan

Tsige yan majalisar PDP 23: Gwamnan Filato ya ziyarci Tinubu, ya yi karin bayani

EFCC ta dade tana saka ido kan Obiano

An dai fara kama tsohon gwamnan ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas a ranar 17 ga Maris, 2022, a lokacin da yake shirin shiga jirgi zuwa birnin Houston na kasar Amurka.

An kama shi ne da misalin karfe 8:30 na dare, sa’o’i bayan ya bar mukamin gwamna, wanda hakan ya sa ya rasa kariya daga kama shi da kuma gurfanar da shi gaban kuliya.

Ya kasance a cikin jerin sunayen masu laifi da EFCC ke sakawa ido na wani lokaci kafin daga bisani a kama shi bisa zargin cin hanci da rashawa.

Yan sanda sun kama makanike da ya tsere da motar kwastoma

A wani labarin kuma, rundunar 'yan sanda ta ce ta samu nasarar kama wani dattijo da ke sana'ar kanikanci bisa zargin ya sace motar kwastomansa a jihar Legas

An ruwaito cewa makaniken ya je har gidan kwastoman bayan ya tafi coci, inda ya karbi makullin motar daga hannun 'yar mutumin, ya sace motar

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel