Buba Galadima Ya Yi Maganar Ficewar Kwankwaso Daga NNPP Zuwa APC da Takarar 2027

Buba Galadima Ya Yi Maganar Ficewar Kwankwaso Daga NNPP Zuwa APC da Takarar 2027

  • Zuwa yanzu Rabiu Musa Kwankwaso bai janye kafarsa daga jam’iyya mai alamar kayan dadi ba
  • Buba Galadima ya musanya rade-radin cewa APC za ta karbe ‘dan takaran shugaban kasar NNPP
  • Jigon na jam’iyyar NNPP ya yi karin haske a kan jita-jitar da ya yi hira ta musamman da Legit

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Ana ta rade-radin akwai yiwuwar Rabiu Musa Kwankwaso ya yi tsalle zuwa jam’iyyar nan ta APC mai mulkin Najeriya.

Legit Hausa tayi magana da Buba Galadima wanda babban jigo ne a jam’iyyar NNPP kuma na-kusa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Rabiu Kwankwaso
Buba Galadima yace Rabiu Kwankwaso yana NNPP Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Hirar Buba Galadima da Legit

Injiniya Buba Galadima ya shaida mana zuwa yanzu babu wata magana da aka yi da ‘dan takaran shugaban kasar kan dawowa APC.

Kara karanta wannan

Rikicin siyasar Kano: Ganduje ya tura sako mai muhimmanci game da alakarsa da su Kwankwaso

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A hirar da muka yi da babban ‘dan siyasar, yace mutane ne suka fassara abin da ya faru da Bola Tinubu ya hadu da Abdullahi Ganduje.

Galadima yake cewa shugaban kasar ya nunawa shugaban APC na kasa ya sasanta da tsohon mai gidansa bayan hukuncin kotun koli.

Tsohon jigon na APC ya yi ikirarin Tinubu ya dauki matsayar ne bayan an tabbatar masa NNPP tayi nasara a zaben jihar Kano a 2023.

Kwankwaso zai koma APC daga NNPP?

"A gaskiyar magana babu wata magana da aka yi na komawar Rabiu Kwankwaso zuwa jam’iyyar APC.
"Muna ji mutane suna magana musamman da shugaban APC na kasa ya dauki mukarrabansa wajen Bola Tinubu."

- Rabiu Musa Kwankwaso

Takara da mulkin Kwankwaso na Allah SWT ne

Da yake magana da Legit, Galadima yace Rabiu Kwankwaso yana nan a jam’iyyar NNPP, kuma idan Allah SWT ya nufa, zai yi mulkin kasa.

Kara karanta wannan

Ni zan zama shugabanka da zarar ka shigo APC, Ganduje ya fadawa Kwankwaso

‘Dan siyasar yace suna zargin an yi murdiya a zaben 2023 domin sun gano an yi wa NNPP magudin kuri’u fiye da 100, 00 a jihar Nasarawa.

A Bauchi, bincikensu ya nuna masu an yi wa jam’iyyar NNPP cogen kuri’u kusan 160, 000 a wasu kananan hukumomi a takarar shugaban kasa.

2023: Galadima ya ce an yi wa Kwankwaso magudi

"Ina fada maku idan Allah SWT ya yi Kwankwaso zai yi mulkin Najeriya, zai yi. Ka da a damu da ya samu kuri’u miliyan 1.5 a 2023.
"Wannan abin da hukumar INEC ta fada ne kurum. da haka Buhari ya fara (nasara a jihar Nasarawa kurum a 2011), har ya samu mulki."

- Buba Galadima

'Yan APC sun ce a dawo da Kwankwaso

Ana da labari wasu da sunan matasan APC sun fara huro wuta a tsige Abdullahi Umar Ganduje kuma a hana shi mukami a gwamnati.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da za su faru da NNPP da APC idan Abba, Kwankwaso suka sauya-sheka

Shugabannin APC na jihar Kano sun zargi ‘Yan Kwankwasiyya da shiga rigar jam’iyya domin ganin bayan Dr. Abdullahi Ganduje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel