Wahalar Rayuwa: Ka da a Karaya da Mulkin Bola Tinubu, Jigon APC Ya Lallabi Mutane

Wahalar Rayuwa: Ka da a Karaya da Mulkin Bola Tinubu, Jigon APC Ya Lallabi Mutane

  • Wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye ya roki ‘yan Najeriya su kara hakuri da yadda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ke mulkin kasar nan
  • Dan siyasar ya ce matakan da aka dauka da cire tallafin mai da sauran matakai za su taimaka ne wajen gina tattalin arziki mai karfi a nan gaba kamar yadda shugaban ke fata
  • Ya shawarci ‘yan kasar nan da kada su karaya da mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, domin lamura za su inganta da zarar kudurorin sun kankama yadda ya dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Osun- Wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye ya roki ‘yan Najeriya su kara hakuri da yadda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ke tafiyar da mulkin kasar nan.

Kara karanta wannan

"Wannan ai sata ce," NLC ta magantu kan karin kudin wutar lantari a Kogi

Olatunbosun Oyintiloye wanda da shi aka yi fafutukar gangamin neman zaben Tinubu, ya ce shugaban cikakkiyar dan kasa ne mai kishi da zai tabbatar da cika dukkanin alkawuran da ya daukarwa ‘yan kasar nan.

Bola Ahmed Tinubu
Jigon APC za ce za a dadi a mulkin Buhari Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ya kara da cewa duk da matakin da gwamnati ke dauka a yanzu, kamar su cire tallafin man fetur na haddasa wahalhalu ga ‘yan kasa, nan gaba kadan matakan za su samar da ginshiki mai kwari na bunkasar tattalin arziki, kamar yadda This Day ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sai an jure za a ji dadi,” Oyintiloye

Tsohon dan majalisa kuma jigo a jam’iyyar APC, Olatunbosun Oyintiloye ya bayyana wahalar da ‘yan Najeriya ke sha na dan lokaci ne.

Ya bayyana haka ne ga manema labarai a jihar Osun inda ya ce sai an sha wuya a kan sha dadi.

Kara karanta wannan

Dalibai 14 cikin 24 da aka sace a jami'ar Kogi sun kubuta, 'yan sanda sun yi bayani

Jigon APCn ya bayyana cewa wannan na daga cikin saudaukarwar da ‘yan Najeriya za su yi idan suna son ci gaban kasarsu, kamar yadda The Cable ta wallafa.

A kalamana:

” Manufofin shugaban kasa masu kyau ne ga Najeriya, dole sai mun shirya sadaukarwa, kuma abin da ake fuskanta ke nan yanzu.”

Ya shawarci ‘yan kasar nan da kada su karaya da mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, domin lamura za su inganta a nan gaba.

Kaya za su tashi a zamanin Tinubu

A baya mun baku labarin cewa kaya hukumomin kasar nan sun samar da sabon fasalin haraji ga masu shigo da kaya cikin kasar nan ta tashoshin ruwa.

Wannan mataki na zai kara tsadar farashin kayayyakin da aka shigo da su kamar motoci da wayoyin hannu a lokacin da Naira ta fara daikar saiti a kasuwar canji.

Muhammad Malumfashi, babban editan sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.