"Shi Ba Dan Jihar Nan Ba Ne": Wike Ya Bayar da Karin Haske Kan Rikicinsa da Gwamna Fubara

"Shi Ba Dan Jihar Nan Ba Ne": Wike Ya Bayar da Karin Haske Kan Rikicinsa da Gwamna Fubara

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce sansaninsa ya amince da duk wani mataki da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka dangane da rikicin siyasar Rivers
  • Wike ya ce ba zai ba sarakunan gargajiya a jihar Rivers da kuma magoya bayansa kunya ba
  • Wike, wanda shi ne tsohon gwamnan jihar mai arziƙin man fetur, ya sha takun saka tsakaninsa da Gwamna Siminalayi Fubara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Port Harcourt, jihar Rivers - Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, ya yi magana kan rikicinsa da Gwamna Siminalayi Fubara.

Wike ya bayyana cewa sansaninsa ya cika nasu ɓangare na yarjejeniyar zaman lafiya da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ƙaddamar wacce dukkanin ɓangarorin da ke da ruwa da tsaki a rikicin siyasar jihar suka amince da ita.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamnan Abba ya faɗi gaskiya kan tsoma bakin Shugaba Tinubu a hukuncin kotun ƙoli

Wike ya magantu kan rikicinsa da Fubara
Wike ya ce ya cika sharudan da aka gindaya kan rikicinsa da Gwamna Fubara Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS, Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Wike, tsohon gwamnan jihar Rivers, yayi magana a ranar Asabar, 13 ga watan Janairu, lokacin da ya ziyarci Eze Nnam Obi III, Oba na Ogbaland a ƙaramar hukumar Ogba/Egbema/Ndoni ta jihar Rivers.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mun yarda da yarjejeniyar zaman lafiya": Wike

Ministan ya shaida wa sarkin cewa ya damu da zaman lafiya a jihar kuma ba zai ɓata masa rai ba (sarkin), kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

A halin yanzu Wike yana takun saƙa tsakaninsa da Siminalayi Fubara, gwamnan jihar Rivers mai ci.

Fitaccen ɗan siyasar na Rivers ya bayyana cewa:

"Shi (Shugaba Tinubu) ba ɗan jihar nan ba ne, don haka mutane da yawa sun gudanar da al’amuran ƙasar nan, rikici ya dabaibaye wasu jihohi, da kyar ka ga wani ya fito ya ce ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasa ba, ‘Ina buƙatar zaman lafiya a cikin jihar."

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da ƴan bindiga suka bankawa fadar fitaccen basarake wuta a Najeriya

Wike ya ci gaba da cewa:

"Mun amince da duk wani mataki da Shugaban ƙasa Tinubu ya ɗauka kuma a namu ɓangaren mun cika duk wani sharaɗi da shugaban ƙasa ya bayar domin na faɗa muku ba zan ba ku kunya ba.
"Don kawai sanar da ku cewa buƙatar ku na tabbatar da cewa an samu zaman lafiya a jiha da kuka nemi shugaban ƙasa ya sa baki, mun amince."

Na Hannun Daman Wike Ya Yi Murabus

A wani labarin kuma, kun ji cewa Chidi Amadi, Shugaban maika'atan Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas, ya yi murabus daga kan kujerarsa.

Kwamishinan labarai da sadarwa na jihar Ribas, Joseph Johnson, ya tabbatar da murabus ɗin Amadi wanda na hannun daman Nyesom Wike ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel